Mutane Sun Fusata Yayin da Ake Zargin Wani Mutumi Ya Yi Ɓatanci Ga Annabi SAW a Jihar Arewa

Mutane Sun Fusata Yayin da Ake Zargin Wani Mutumi Ya Yi Ɓatanci Ga Annabi SAW a Jihar Arewa

  • Zanga-zanga ta barke a wani ƙauyen karamar hukumar Ɓatagarawa a Katsina kan zargin wani ya yi kalaman ɓatanci
  • Rahoto ya nuna mutumin mai suna, Mani Habu, ya yi rubutun ɓatanci a Facebook, inda ya nuna tantama kan Alƙur'ani
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma ta ɗauki matakan kwantar da duk wata tarzoma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Katsina - An fara zaman ɗar-ɗar da fargaba a jihar Katsina bayan wani kirista mai suna, Mani Habu, ya yi rubutu mai cike da ruɗani a shafin Facebook.

Kalaman da mutumin ya wallafa ya jawo tashin hankali a garin Katsina saboda ana ganin ɓatanci ne ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.

Sufetan yan sanda na ƙasa.
Mutane Sun Fusata Yayin da Ake Zargin Wani Mutumi Ya Yi Ɓatanci Ga Annabi SAW Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Habu ya fito daga kauyen Sabon Garin Alhaji Yahuza a karamar hukumar Batagarawa da ke cikin jihar Katsina, in ji Channels tv.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana ƴan takarar da yake goyon baya a zaben da za a yi ranar Asabar a jihohi 9

Jaridar Punch ta tattaro cewa lamarin ya ƙara zafi ne yayin wasu gungun mutane cikin fushi suka bankawa gidansa da motarsa wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargi da ɓatancin ya samu ya arce daga gidansa da ke Babbaruga kafin fusatattun mutanen su ƙarisa.

Wane kalaman ɓatanci mutumin ya yi?

Kalaman batanci da ake zargin mutumin ya yi wanda a yanzu aka goge daga Facebook, ya yi ikirarin cewa Musulunci ba shi da tushe kuma ya sanya ayar tambaya kan asalin Alkur'ani.

Habu ya bayyana cewa ba Annabi Muhammad SAW ne ya rubuta Alkur’ani ba kuma ya zargi wasu sahabbai da kirkiro shi.

Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, koda yake Habu da iyalansa sun yi nasarar tserewa zuwa inda ba a sani ba.

"Lamarin ya yi kamari ne yayin da wasu fusatattun mutane suka kona motar Habu da gidansa a Unguwar Babbarruga,” inji shi.

Kara karanta wannan

Dirama yayin da kotu ta hana cafke shugaban ma'aikatan gwamnan PDP kan abu 1 tak

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq ya fitar ranar Alhamis.

Ya ce lamarin ya afku ne ranar 30 ga watan Janairu, lokacin da DPO na Ɓatagarawa ya samu kiran gaggawa cewa zanga-zanga ta ɓarke a Sabon Garin Alhaji Yahuza.

Kakakin ƴan sandan ya ce:

"Bayan samun rahoto, nan take aka tura dakarun ƴan sanda zuwa wurin kuma sun kwantar da hankula tare da daƙile zanga-zangar.
"Bayan haka kuma kwamishinan ƴan sanda ya gana da kwamishinan addinai, sarakuna, malamai da sauran masu ruwa da tsaki, inɗa ya buƙaci su taka wa mabiyansu birki.
"An ƙara ɗaukar matakan domin tabbatar da tsaro a kauyen, sannan rundunar ƴan sanda na kira ga duk mai bayanan da zasu taimaka wajen bincike ya kawo mata."

Babu hannun gwamnati a kama Dutsen Tanshi

Kara karanta wannan

Mangu: An kashe bayin Allah 91 yayin da wasu 158 suka ji raunuka a rikicin da ya ɓarke a jihar arewa

A wani rahoton kuma Gwamnatin Bauchi ta musanta hannun Gwamna Bala Mohammed a cafke fitaccen malamin nan, Sheikh Idris Dutsen-Tanshi.

Malamin mai ikirarin bin tafarkin aƙidar Sunnah na fuskantar shari'a a gaban kotu wanda ya kai ga kulle shi a gidan Kurkuku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel