“Talaka Na Shan Wuya”: Jerin Jihohi 10 da Suka Fi Tsadar Kayan Abinci, Kogi Ce a Gaba

“Talaka Na Shan Wuya”: Jerin Jihohi 10 da Suka Fi Tsadar Kayan Abinci, Kogi Ce a Gaba

  • Duk da kokarin gwamnati na ganin rayuwa ta yi sauki, an gano 'yan Najeriya a yanzu na siyen abinci da tsada fiye da a shekarar 2023
  • Rahoton NBS ya bayyana jerin jahohin Najeriya da hauhawar farashin kayan abinci ke kara lulawa sama yayin da jama'a ke kukan 'babu'
  • A zantawar Legit Hausa da dan kasuwa, Nurudden Mohammed daga jihar Kaduna, ya bayyana mana farashin shinkafa da taliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci a watan Mayun 2024 ya karu zuwa kashi 40.66.

Sabon alkalamin hauhawar farashin abinci ya nuna karuwar farashin da kashi 115.84 idan aka kwatanta da farashin a watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam za ta dauki matakin da zai kawo saukin kayan abinci a Najeriya

NBS ta fitar da jadawalin farashin abinci a Najeriya
Sayen kayan abinci na ci gaba da zama babban aiki ga 'yan Najeriya saboda tsada. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Hukumar NBS ta ruwaito farashin abinci na wata wata ya nuna raguwar farashin a watan Mayun 2024 da kashi 0.22 idan aka kwatanta da farashin a watan Afrilun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kayayyakin da suka jawo tsadar abinci

Rahoton ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci na shekara-shekara ya biyo bayan karin farashin wasu kayayyaki.

Hukumar ta NBS ta lissafa kayayyakin abincin da suka hada da garin semovita, garin dawa, garin kwaki, wake, dankalin Turawa, doya, da rogo.

Sauran sun hada da man ja da man gyada, dangin kifaye (kamar tarwada, karfasa); naman dabbobin gida, kaji, da naman daji.

Jerin jihohi 10 mafi tsadar kayan abinci

Ga jerin jihohin Najeriya mafi fama da hauhawar farashin abinci a cikin watan Mayun 2024.

Jihar Kogi: 46.32%

Kogi ke kan gaba a jihohin Najeriya mafi tsadar kayan abinci a daidai lokacin da take fama da kalubalen tsaro da kuma rigimar manoma da makiyaya.

Kara karanta wannan

Rahoton NBS: Jigawa da jerin jihohin Najeriya da suka fi tsadar man fetur a watan Mayu

A shekarun da suka gabata, noma ya kasance mabuɗin ci gaban tattalin arzikin Kogi, amma a ƴan watannin nan, rayuwa ta tsananta ga mazauna jihar sakamakon sayan abinci da tsada.

Jihar Ekiti: 44.94%

Ekiti ita ce jiha ta biyu da aka fi samun hauhawar farashin abinci a watan Mayun 2024, duk da cewa tana da kasa mai albarkar noma.

Yanzu dai ya zama wajibi Gwamnan Biodun Oyebanji ya lalubo hanyar da zai yi amfani da ita wajen dawo da harkar noma a jihar domin rage farashin kayan masarufi.

Sauran manyan jihohi 10 da ke da hauhawar farashin kayan abinci suna cikin wannan jadawalin na a ƙasa:

MatsayiSunayen jihohiFarashin abinci a Mayu, 2024
Jiha ta 3Kwara44.66%
Jiha ta 4Osun44.57%
Jiha ta 5Edo44.42%
Jiha ta 6Enugu44.42%
Jiha ta 7Imo44.32%
Jiha ta 8Cross River 44.24%
Jiha ta 9Abia 44.02%
Jiha ta 10Akwa Ibom43.83%

Kara karanta wannan

"Dalilai 5 da suka sanya Abacha ya fi sauran shugabannin Najeriya nagarta"

Farashin shinkafa da taliya a Kaduna

A zantawar mu da Nurudden Mohammed, dan kasuwa a jihar Kaduna, ya bayyana cewa yanzu ana sayar da buhun shinkafa yar gida N70,000 zuwa N72,000 sabanin N67,000 zuwa N68,000 da aka siyar a watan Mayu.

Haka zalika, Nurudden ya ce yanzu haka ana sayar da katan na taliya a kan N16,000 sabanin N15,800 da aka siyar a watan Mayu.

Wadannan farashin a cewar dan kasuwar sun shafi kayan kamfanonin da aka fi saye ne, amma farashin ya haura hakan a kan wasu kamfanoni, ko kasa da hakan a wasu.

Tinubu ya nada shugaban hukumar BPE

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar hukumar kamfanonin gwamnati (BPE).

Shugaba Tinubu ya amince da nadin Mista Ayodeji Ariyo Gbeleyi, wanda tsohon kwamishinan kudi ne na jihar Legas a matsayin shugaban BPE.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.