Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Sake Daukar Matakin Karya Farashin Abinci a Nijeriya

Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Sake Daukar Matakin Karya Farashin Abinci a Nijeriya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ya sake daukar matakin karya farashin abinci a Nijeriya ta hanyar fitar da hatsi daga rumbun gwamnati
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce Tinubu ya bayar da umarnin fitar da ton 42,000 na kayayyakin abinci domin rabawa talakawa
  • Idris ya ce ton 42,000 na kayan abinci da za a fitar sun hada da masara (ton 23,600), dawa (ton 12,860), gero (ton 3,700), da garri (ton 1,840)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kaddamar da shirin fitar da ton 42,000 na kayayyakin abinci daga rumbun ajiyar abinci na kasa (NSFR) domin raba wa jihohi.

Tinubu ya dauki matakin karya farashin kayan abinci
Ministan yada labarai ya ce Tinubu ya damu kan yadda tsadar abinci ta karu a Nijeriya. Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

Za a raba abincin a fadin kasar ga marasa galihu domin rage masu radadi na tsadar rayuwa da ake ciki a Nijeriya.

Kara karanta wannan

CBN ya sake daukar mataki na karya Dala, 'yan canji za su samu $10,000 kan N1,101/$1

Kayan abincin da Tinubu ya fitar

Wannan rabon na gwamnatin tarayya, an gudanar da shi ne a ranar Lahadi, a gidan gwamnatin Sokoto, jihar Sokoto, kamar yadda talabijin na Arise ya ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ton 42,000 na kayan abincin sun hada da masara (ton 23,600), dawa (ton 12,860), gero (ton 3,700), da Garri (ton 1,840).

Kayayyakin da aka kai jihar Sokoto ya kunshi masara ton 506.00, dawa (ton 589.00), da gero (ton 216.20).

"Tinubu ya damu da tsadar abinci" - Idris

Jaridar Leadership ta rahoto ministan yada labarai na kasa, Mohammed Idris, ya ce rabon hatsin wani shiri ne na gwamnatin tarayya na rage wahalhalun da ke addabar kasar.

Ya ce shugaba Bola Tinubu ya damu da hauhawar farashin kayan abinci kuma ya kuduri aniyar samar da abincin da kuma ganin farashin ya yi araha ga ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

“Mun shiga uku”: Dan Najeriya ya sha tsada bayan siyna katin wutar lantarki na N400,000

A cewarsa, dole ne manufofin shugaban kasar sun jefa 'yan Nijeriya a yanayin matsin rayuwa, amma sannu a hankali kowa zai amfana da tsare-tsaren gwamnatin.

"Talaka zai ji dadi nan gaba" - Idris

“Gwamnati ta yi kira ga 'yan Nijeriya da a ci gaba da hakuri da kara fahimtar manufofinta domin akwai kyakkyawar rayuwa da ke jiranmu nan gaba kadan.
"Kamar yadda kuka sani, shugaban kasa kullum yana bamu tabbacin cewa wandannan matsalolin na karamin lokaci ce, kuma tabbas za mu shawo kan su."

- A cewar Idris.

Da yake jawabi a wajen taron, ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya ce shugaban kasar na da burin ganin an dakile tashin farashin kayayyakin abinci.

Gwamnati ta fara noman abinci

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta fara noman kayan abinci da yawa a kokarinta na ganin ta samar da wadataccen abinci ga 'yan Nijeriya.

Legit Hausa ta ruwaito cewa ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya yi nuni da cewa har sai abinci ya wadata ne farashinsa ke iya karyewa a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel