Fitacciyar Jarumar Fina Finan Najeriya Ta Rigamu Gidan Gaskiya, Masoyanta Sun Yi Jimami

Fitacciyar Jarumar Fina Finan Najeriya Ta Rigamu Gidan Gaskiya, Masoyanta Sun Yi Jimami

  • An shiga jimami a masana'antar shirya fina-finan Kudancin Najeriya (Nollywood) yayin da jaruma Stella Ikwuegbu, ta mutu
  • Ta mutu ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, yayin da ‘yan uwa da abokan aikinta ke taron jimamin mutuwarta a gidanta
  • Stella Ikwuegbu ta shiga harkar fim ne a shekarar 1990 kuma ta fito a fina-finan da suka hada da Ukwa, Spoiler da Madam Koikoi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jarumar Nollywood, Stella Ikwuegbu ta rigamu gidan gaskiya a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, kuma mutuwarta ta jefa abokan aikinta, masoyanta, da 'yan uwanta cikin jimami.

Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Stanley Nwoko, wanda aka fi sani da Stanley Ontop, ya fitar da sanarwar mutuwar Stella Ikwuegbu a jiya Lahadi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bukaci daraktan hukuma dan Arewa da Buhari ya nada ya yi murabus

Jarumar Nollywood, Stella Ikwuegbu ta kwanta dama
An shiga jimami bayan samun labarin mutuwar jarumar Nollywood, Stella Ikwuegbu. Hoto: @stanley_ontop
Asali: Instagram

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram, Ontop ya bayyana cewa Stella ta mutu ne sakamakon ciwon daji da ya cinye kafarta kuma mutuwarta ta jefa mutane cikin jimami.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarumar fim, Stella Ikwuegbu ta mutu

Stanley Ontop ya wallafa cewa:

"Shahararriyar 'yar wasan fina-finan Nollywood, Misis Stella Ikwuegbu ta mutu.
"Tsohuwar Jarumar ta bar duniya a yau bayan ta yi fama da cutar kansar kafa."

Wacece Stella Ikwuegbu?

Jarumar da ta rasu ta fito daga jihar Enugu. Ta yi karatun digiri a Makarantar koyon gudanarwar aiki da fasaha (IMT) da ke Enugu.

Ta shiga masana'antar a cikin 1990 kuma ta fito a cikin fina-finai da yawa da suka hada da Ukwa, Spoiler, Madam Koikoi, Sound of Love, Holy Man, and Two Hearts.

Baya ga kasancewarta ‘yar wasan kwaikwayo, ta kuma mallaki wani gidan abinci mai suna The Film Bar.

Kara karanta wannan

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ya riga mu gidan gaskiya

Duba sakon da Stanley ya fitar a kasa:

Jarumin Nollywood, Amaechi Muonagor ya mutu

A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa fitaccen jarumin Nollywood, Amaechi Muonagor ya rigamu gidan gaskiya.

Marigayin ya mutu ne a yau Lahadi 24 ga watan Maris bayan ya sha fama da jinyar cutar hanta na tsawon lokaci.

An haifi jarumi Muonagor a ranar 20 ga watan Agustan 1962 a karamar hukumar Idemili a jihar Anambra wanda ya karar da duk abin da ya mallaka wajen neman magani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel