Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya Ta Yanke Jiki Ta Faɗi Ta Mutu a Yayin Da Ta Ke Shara a Wurin Ibada

Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya Ta Yanke Jiki Ta Faɗi Ta Mutu a Yayin Da Ta Ke Shara a Wurin Ibada

  • Jarumar Fina-fina ta Nollywood, Chinedu Benard ta riga mu gidan gaskiya.
  • Benard ta yanke jiki ta fadi ta mutu ne yayin da ta su ke aikin tsaftace coci a Enugu
  • Shugaban kungiyar jaruman fina-finai, AGN, Emeka Rollas ya tabbatar da rasuwar Benard

Jihar Enugu - Likitoci a asibitin East Side a Jihar Enugu sun tabbatar da mutuwar jarumar fina-fina ta Nollywood, Chinedu Bernard.

Ta yanke jiki ta fadi ne a yayin da ta ke aikin tsaftace coci na St. Leo the Great Catholic Church da ke rukunin gidajen Tarayya a jihar.

Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya Mutu a Yayin Da Ta Ke Shara a Wurin Ibada
Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya Mutu a Yayin Da Ta Ke Shara a Coci. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

A cewar rahoton The Punch, faston cocin, Rabaran Fada Uchendu Chukwuma, da wasu masu ibada a cocin, sun garzaya da ita asibitin a inda aka tabbatar ta rasu.

Kara karanta wannan

Kotu ta jefa Ma'aikatan banki 2 kan laifin sace miliyoyin kudi na kwastoman da ya mutu

A cewar wani rubutu da daya daga cikin masu aiki a cocin ya wallafa, ana kokarin tuntubar yan uwanta kafin a kai gawarta dakin ajiye gawa a asibiti.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jarumar da aka fi sani da Choco ta fito a fina-finai da suka hada da ‘The Mad’, ‘Money Fever’, ‘The Big Mama’s Stick’, ‘The Last Manhood’ da ‘Mad Love’.

Shugaban kungiyar jaruman fina-finai, AGN, Emeka Rollas ya tabbatar da rasuwar Benard

Emeka Rollas, Shugaban kungiyar jaruman fina-finai, AGN, ya yi ta'aziyya mai ratsa jiki game da rasuwar Chinedu Benard da wata jarumar Chima Precious.

Emeka ya ce yana daf da magana a kan auren mata biyu da jarumi Yul Edochie ya yi ne sai ya samu labarin rasuwar jaruman biyu.

Ya wallafa ta'azziyar a shafinsa na Instagram kuma ya bukaci al'umma su saka su a addu'a.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga, sun ceto wasu mata, sun kwato AK47

An Tsinci Gawar Jarumar Fim Ta Najeriya a Ɗakin Otel Sati Ɗaya Bayan Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarta

A wani labarin daban, An tsinci gawar Jaruma Takor Veronica a cikin wani daki na Otel a Jihar Benue, kamar yadda The Nation ta rahoto.

A cewar rahotanni daban-daban, an gano gawar na Veronica ne kimanin sati baya bayan ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta.

An rahoto cewa an tsinci gawarta ne a wani dakin otel a unguwar Nyinma na Makurdi.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel