Hanyoyin da za abi domin kare kai daga cutar hawan jini
Wasu masana sun bayyana wasu muhimman hanyoyi da ya kamata mutane su rinka bi domin kare kai daga kamuwa daga cutar hawan jini, wacce ta zama tamkar ruwan dare a wannan lokacin
Wasu masana a fannin kimiyya a Najeriya, sun bayyana wasu hanyoyi da ya kamata mutane su dinga bi wanda zasu taimaka wurin kaucewa kamuwa da cutar hawan jini.
Wasu daga cikin abubuwan da masanan suka bayyana sun hada da yawan motsa jiki, cin abinci mai gina jiki, da kuma daina cin abincin turawa na gwangwani, saboda masanan sun gano cewa akwai gishiri sosai a cikin abincin.
Wani babban likita dake zaune a babban birnin tarayya Abuja, mai suna Dr. Bashir Mijinyawa, ya bayyanawa manema labarai cewa, bayan wadannan abubuwa da aka lissafo a sama, ana bukatar mutane su dinga yawaita yin bacci da kuma samun isashen hutu, sannan kuma su dinga ragewa kansu damuwa.
Likitan ya bayyana cewa, a wannan lokacin ana ta kara samun masu cutar hawan jini a Najeriya, saboda a wani bincike da aka yi ya nuna cewa a cikin kowanne mutum 100, ana samun kimanin mutane 10 da suke dauke da cutar.
Likitan ya kara da cewa ba sosai aka fiya warkewa daga cutar ba, sai dai kawai mutum ya dage da shan magunguna.
KU KARANTA: Dalilai 6 dake hana matasa aure a Najeriya
Hakazalika, likitan ya bayyana cewa, mutane da suke dauke wannan cuta, a lokuta da dama takan zame musu matsala, inda za ta dinga sanya musu ciwon zuciya, ko ciwon koda ko kuma rabin jikinsu ya shanye. Sannan a lokuta da dama ciwon yakan bata wasu hanyoyi da jini yake bi a jikin dan adam.
Likitan ya bayyana cewa, bisa la'akari da yanayin abubuwan da cutar take haifarwa, yana da mutukar muhimmanci masu cutar su dinga zuwa asibiti a lokuta da dama domin a dubasu, musamman ma wadanda suka gaji cutar a wurin iyayensu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana
Asali: Legit.ng