Bayan An Koka da Nade Nadensa, Tinubu Ya ba Amininsa Mukami a Gwamnatin Tarayya

Bayan An Koka da Nade Nadensa, Tinubu Ya ba Amininsa Mukami a Gwamnatin Tarayya

  • Bola Ahmed Tinubu ya saurari koke-koken al’umma, ya canza ‘yan kwamitin gudanarwa a manyan makarantun gwamnati
  • Shugaban kasar ya ba Bisi Akande wanda amininsa ne mukami a gwamnatin tarayya da ya tashi rabon kujeru wannan karo
  • Wole Olanipekun wanda ya tsayawa Tinubu da ake gwabzawa a shari’ar zaben shugaban kasa ya samu matsayi a UNILAG

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya amince da wasu nade-naden mukamai a sakamakon korafi da ya biyo bayan abin da aka yi a baya.

Mai girma shugaban kasar Najeriya ya canza mutanen da za su rike majalisun gudanar da harkokin jami’o’i da manyan makarantu.

Bisi Akande da Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba Bisi Akande matsayi a Gwamnatin Tarayya Hoto: www.bisiakande.com
Asali: UGC

Bola Tinubu ya tura Bisi Akande UI

The cable ta ce Bisi Akande yana cikin mutum 255 da suka samu mukamai a manyan makarantun gaba da sakandaren gwamnati.

Kara karanta wannan

Bayan tsige Mamman Ahmadu, Tinubu ya ba tsohon kwamishinan Legas wani babban muƙami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Nnamdi Mbaeri ya sanar a wani jawabi, Cif Bisi Akande zai jagoranci majalisar gudanar da harkokin jami’ar Ibadan.

Alakar Akande da shugaba Tinubu

Bisi Akande wanda ya yi gwamna a shekarun baya shi ne shugaban farko na APC a tarihi, yana cikin masu kusanci sosai da Bola Tinubu.

Kwanakin baya aka ji shugaba Bola Tinubu ya ba diyar ‘dan siyasar mukami a gwamnati, Temitope Ilori ta zama shugabar NACA.

Gwamnatin Tinubu ta tuno da Wole Olanipekun

Shi kuma lauyan shugaban kasar a kotun zabe, Wole Olanipekun ya zama shugaban majalisar gudanar da harkokin jami’ar Legas.

Wole Olanipekun SAN ya kare shugaba Bola Tinubu a lokacin da Atiku da Peter Obi suka kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa.

Wasu da Tinubu ya ba mukamai

Sauran manyan APC da suka samu mukami wannan karo sun hada da Adebayo Shittu wanda ya yi minista a mulkin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tanimu Kurfi: Yadda aka shigo da na hannun daman Yar’adua cikin gwamnatin Tinubu

Rahoton Tribune ya tabbatar da tsohon ministan sadarwan ya samu kujera ne a jami’ar kiwon lafiya ta David Umahi da ke jihar Ebonyi.

Tsohon mai ba APC shawara a kan harkokin shari’a, Muiz Banire ya zama shugaban wannan majalisa ta jami’ar sufuri ta garin Daura.

An koka da mulkin Bola Tinubu

Rahoto ya zo cewa Malam Kasim Balarabe Musa ya jagoranci zanga-zangar lumunar da aka shirya a ranar 12 ga watan Yunin 2024.

Yaron tsohon gwamnan na Kaduna ya ce ba a taba samun abubuwa sun tabarbare kamar yau ba, ya ba Bola Tinubu shawarar murabus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel