Ana Shirin Babbar Sallah: An Sake Cafke Wasu Barayin Raguna a Abuja, an Samu Bayanai

Ana Shirin Babbar Sallah: An Sake Cafke Wasu Barayin Raguna a Abuja, an Samu Bayanai

  • Dubun wasu barayi ta cika bayan da aka kama su a lokacin da suke kokarin sayar da wasu raguna biyu da aka sato a gidan wani Alhaji
  • An ruwaito cewa an kama mutanen biyu ne a kasuwar dabbobi ta Gwagwalada da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis
  • A zantawar mu da Auwalu Bala, wani mai sayar da dabbobi a Katsina, ya ce dabbobi sun yi kwantai babu mai su saya a sallar nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An kama wasu mutum biyu a lokacin da suke kokarin sayar da wasu raguna da ake zargin sun sato a kasuwar dabbobi ta Gwagwalada da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"Mene nayi muku?": Sanata ta koka kan mayar da ita saniyar ware a mazaɓarta kan kudi

Wannan na zuwa ne kasa da awanni 48 bayan kama wasu mutum biyu dauke da shanu na sata a kasuwar dabbobi ta Abaji da ke babban birnin tarayyar.

An kama barayin raguna a Abuja
An kama mutum 2 suna kokarin sayar da ragunan sata a Gwagwalada, Abuja. Hoto: Sani Hamza Funtua
Asali: Original

An sace wa Alhajin Abuja raguna

Wani ganau ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa ana zargin wadanda aka kama sun sato ragunan ne daga gidan wani Alhaji Rabiu Usman a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce shi Alhaji Rabiu Usman ya siyo dabbobin ne domin ya yi layya da su a gidansa da ke Unguwar Dodo, a kwaryar Abuja.

Ya bayyana cewa:

"Alhaji Rabiu abokina ne. Tare da ni aka je kasuwar Madalla makon jiya inda ya sayi ragunan biyu ya daure a gida, amma a ranar Laraba ya sanar da ni an sace ragunan."

Yadda aka kama barayin ragunan Alhaji

Ganau din ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Malawi: Jirgin mataimakin shugaban ƙasa ya yi hatsari, mutanen ciki sun mutu

"Alhaji Rabiu ya sanar da 'yan kasuwar dabbobi a Gwagwalada kan sace ragunansa. Misalin karfe 5 na yamma, aka kira shi a kan ya ne ya duba wasu raguna da aka kawo za a sayar.
"Ko da ya isa wajen, sai kuwa ya tarar ragunan nasa ne da aka sace. Wannan ya sa aka sanar da 'yan sa-kai da ke a cikin kasuwar inda suka kama wadanda ake zargin."

Har zuwa kammala wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Abuja, SP Adeh Josephine kan lamarin ba.

'Yan kasuwar dabbobi sun dauki mataki

A zantawarmu da wani mai sayar da dabbobi a kasuwar Sheme da ke jihar Katsina, Auwalu Bala, ya bayyana cewa an daina sayen dabbobi daga hannun wanda ba a san shi ba a kasuwar.

Auwalu Bala ya shaida cewa lokuta da dama ana samun wasu su zo sayar da dabbobin sata, kuma a kama su tare da mika su ga hukuma, yayin da 'yan kasuwa ke kaffa-kaffa da sayen kayan sata.

Kara karanta wannan

Barayi sun haura gida sun yi ta’asa, an sacewa bayin Allah ragon layya a Abuja

Dabbobi sun wadata, amma sun yi tsada

Dangane da farashin dabbobin layya a bana, Auwalu Bala ya yi korafin yadda raguna, shanu da awakai suka yi kwantai, duk da cewa ba a tsawwala masu kudi ba.

Sai da a nan jihar Kaduna, mun ji ta bakin Alhaji Bashir Manaja, jim kadan bayan ya dawo daga kasuwar dabbobin, wanda ya koka kan yadda aka tsawwala kudin raguna a bana.

A cewar Alhaji Bashir Manaja, karamin rago da a 2023 aka sayar da shi kan N150,000 yanzu ya haura N200,000 yayin da su ma kaji suka yi tsada, inda ake sayar da su N10,000 har zuwa N15,000 da yankin da ya ke.

An kona gawar dan fashi a Abuja

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa wasu fusatattun mazauna karamar hukumar Abaji da ke Abuja sun kona gawar wani dan fashi bayan an kashe wani sufetan 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Duk da dokar hana masu ciki aikin Hajji, Hajiyar Najeriya ta haifi jaririn farko a Makkah

Rahotanni sun ce ‘yan fashin sun kai farmaki wani banki a garin da misalin karfe 5:30 na yamma bayan sun farmaki ofishin rundunar 'yan sandan karamar hukumar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel