Babbar Sallah: Farashin Ragunan Layya sun yi tashin doron Zabuwa a Garin Abuja

Babbar Sallah: Farashin Ragunan Layya sun yi tashin doron Zabuwa a Garin Abuja

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, al'umma sun koka kan tsadar gami da tashin doron zabuwa na farashin ragunan layya a manyan kasuwanni dake garin Abuja yayin da bikin babbar Sallah ke ci gaba da karatowa.

Sanin kowa ne cewa al'ummar Musulmi a fadin duniya na gudanar da wannan biki na layya cikin a kowace shekara bisa wani tsari gami da tafarki na ibada domin bauta ga Allah Madaukakin Sarki.

A sanadiyar gabatowar wannan babbar rana, bincike da manema labarai na jaridar Vanguard suka gudanar a Kasuwar dabbobi ta Deidei da kuma Dutse ya bayyana cewa, farashin kananan raguna, matsakaita da kuma manya a kasuwannin biyu su na tsakanin N35, 000, N60, 000 da kuma N100, 000.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, da yawan al'umma sun bayyana rashin dadin dangane da tsadar dabbobin a kasuwanni biyu, inda wasu da dama suka dauki dangana da cewar sun hakura da layya a wannan shekara.

Babbar Sallah: Farashin Ragunan Layya sun yi tashin doron Zabuwa a Garin Abuja
Babbar Sallah: Farashin Ragunan Layya sun yi tashin doron Zabuwa a Garin Abuja

A yayin ganawa da wani Dattijo, Mallam Isa Nanono da ya ziyarci kasuwar domin sayen ragunan layya ya bayyana cewa, ya zo kasuwar ne da niyyar sayen babban rago da sai dan karami ya iya saye sakamakon tsadar da dabbobin ke yi a wannan lokaci.

Legit.ng ta fahimci cewa, wasu daga cikin al'ummar dake da niyyar sayen raguna sun yi kira ga gwamnati akan ta kawo dauki cikin wannan babbar matsala da muddin ba haka ba sayen ragunan layya za su gagara a shekaru masu gabatowa.

Kazalika masu sayar da dabbobin sun koka kan rashin samun kasuwa inda wani Mallam Ibrahim Liman ya alakanta wannan matsala da tsadar rayuwa da ta janyo wannan mummunar barazana a kasar nan.

KARANTA KUMA: Saraki ya ziyarci Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel

Ya ke cewa, ta'addanci ya kuma salwantar da dabobi na 'yan kasuwa da dama a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan da ya tursasa su haurawa Jamhuriyyar Nijar da kuma Chadi wajen neman dabbobi da za su ci gaba da gudanar da kasuwancin su.

Ya ci gaba da cewa, kawowa yanzu ko raguna 50 bai sayar ba cikin guda 200 da ya kasa a kasuwar sakamakon tsadar su masu saye ke gujewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng