Babbar Sallah: Dillalan raguna sun fara kokawa, sun ce ga raguna birjik babu mai saye

Babbar Sallah: Dillalan raguna sun fara kokawa, sun ce ga raguna birjik babu mai saye

  • Dillalan raguna sun fara kokawa bisa rashin samun ciniki mai yawa yayin da babbar sallah ta karato
  • Sun bayyana cewa, kasuwarsu ta zama shuru, duk da cewa, saura kwanaki kadan a yi Babbar Sallah
  • Sun kuma ta'allaka rashin cinikin da rashin kudi a hannun mutane, inda suka ce tattalin arzikin ba kyau

'Yan kwanaki kadan kafin gudanar da bikin Babbar Sallah, dillalan ragunan layya sun fara koka rashin ciniki yadda ya kamata a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), wanda ya ziyarci wasu kasuwannin raguna a sassa daban-daban na llorin a ranar Alhamis ya ruwaito cewa dillalan ragunan da dama sun koka da karancin ciniki.

Akwai adadi masu yawa na raguna a dukkan kasuwannin da aka ziyarta, inda dillalan ke jiran masu siye da jiran tsammani.

KARANTA WANNAN: Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Kara karanta wannan

Labari da dumi-dumi: Majalisa ta amince da rokon cin danyen bashin Naira Tiriliyan 4

Babbar Sallah: Dillalan raguna sun fara kokawa, sun ce ga raguna birjik babu mai saye
Raguna a kasuwa | Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: UGC

Kasuwannin da aka ziyarta sun hada da kasuwar shanu ta lpata, kasuwar raguna a babbar kasuwar nan ta Mandate, da kasuwar Adeta, da kasuwar raguna ta Ode Alfa-Nda, da kuma kasuwar raguna ta Zango.

Farashin raguna a kasuwanni

Farashin na raguna sun yi kamanceceniya a kusan dukkanin kasuwanni kasancewar an sayar da mafi kankanin rago tsakanin N35,000 zuwa N40,000 yayin da manyan ragunan suka kasance daga N100,000 zuwa N150,000.

Abdullahi Olufadi, dillalin rago a kasuwar shanu ta Ipata, a wata hira da NAN ya ce dillalan na fuskantar karancin ciniki duk da cewa Babbar Sallah saura ‘yan kwanaki.

Mista Olufadi ya danganta lamarin da rashin kyakkyawan yanayin tattalin arziki a kasar.

A cewar dillalin:

"Zuwa yanzu ya kamata mun yi ciniki mai matukar yawa amma masu saye sukan zo jifa-jifa mutum daya ko biyu suna sayen daya yayin da wasu ba za su iya biyan farashin ba."

Wani lauya kuma mai son siye rago, Tunde Olumoh ya ce bai sayi rago ba har yanzu saboda rashin wadatar kudade.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Mutane sun Koka Kan Yadda Farashin Dabbobin Layya Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

Mazauna garin Kano sun koka da tashin farat ɗaya da farashin rago, shanu da akuya kwanaki kadan kafin bikin sallah babba (Eid-el-kabir), kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa farashin dabbobin ya tashi sosai idan aka hada da farashin su a shekarar da ta gabata.

Alhaji Muslimu Abdulhamid, wani mai sana'ar siyar da rago, yace:

"Ragon da aka siyar N30,000 a shekarar da ta wuce, bana ana siyar da shi tsakanin N55,000-N65,000, na N50,000 ya koma N100,000-N120,000."

KARANTA WANNAN: An sanya dokar takaita zirga-zirga a Katsina saboda shugaba Buhari zai kai ziyara

Korona: Gwamnati ta gargadi Musulman Najeriya game da yawon sallah da zuwa Idi

A wani labarin, Yayin da musulmai masu ke shirin bikin sallah babba a mako mai zuwa, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta yi gargadi game da tafiye-tafiye a lokacin bukukuwan sallah.

Kara karanta wannan

Lagos: 'Yan kasuwa 3 sun sheka barzahu bayan arangama da sojin sama

Shugaban NCDC na Sashin Sadarwa, Dakta Yahya Disu, shi ne ya bayar da wannan gargadin a ranar Laraba yayin shirin karin kumallo na gidan Talabijin din Channels.

Disu ya ce karo na biyu na annobar Korona ta fara ne a Najeriya saboda mutane sun yi tafiya don Kirsimeti a Disambar da ta gabata. Don haka, ya bukaci 'yan Najeriya da su guji tafiye-tafiye marasa mahimmanci a lokacin bukukuwan sallah na mako mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.