Kasuwanni 5 masu arahar dabbobin ileya

Kasuwanni 5 masu arahar dabbobin ileya

Yayin da wasu ke kuka da tsadar dabbobin layya sakamakon karatowar Sallah, wasu kuwa ko a jikinsu domin sanin sirrin kasuwa,

Ga wasu daga cikin kasuwannin da za ka iya sayen dabbobi da araha a Najeriya idan har kana niyyar yin layya ko kiwo.

KU KARANTA KUMA: Masu Rago sun koka da rashin Kasuwa a Kaduna

Kasuwar Shanu ta Wudil a jihar Kano: Rahotanni na cewa kasuwar dabbobi ta Wudil na daya daga cikin tsaffin kasuwanni sayar da shanu da kuma sauran dabbobi cikin sauki. Kasuwar babba ce, kuma tana ci a ranar Juma’a.

Kasuwanni 5 masu arahar dabbobin ileya
Kasuwar Shanu ta Maigatari

Kasuwar Maigatari a jihar Jigawa: Wannan kasuwa ta kasa da kasa ce, kuma kasuwar shanu mafi girma a arewacin Najeria saboda da akwai kimanin shanu miliyan 2 da ake hada-hadarsu a ranar Alhamis da ta ke ci, tana garin Maigari da ke bakin iyakar da Najeriya da Jamhuriyar Niger,  ga mai niyya zai iya samun  Shanu da raguna a rangwamen farashi.

Kasuwanni 5 masu arahar dabbobin ileya
Kasuwar Sheme ta jihar Katsina

Kasuwar Sheme: Daya daga cikin fittattun kasuwannin jihar Katsina, tana karamar hukumar Faskari, kan hanyar Funtua zuwa Gusau, tana kuma ci a ranar Juma’a. Ga mai shawa’a zai iya samun dabbobi kama daga Rakuma da shanu da raguna da Tumakai da Awakai gami da abincinsu da kuma magunguna ga mai aniyar kiwo.

Kasuwar Shanu ta Amansa a Anambra: Wannan kasuwar shanu tana Awka a babban birnin jihar Anambra, ta kuma shahara a yankin gabashin Najeriya. Ga wandanda ke kudu, wannan kasuwa na da saukin dabbobi musamman shanu.

Kasuwanni 5 masu arahar dabbobin ileya
Kasuwar Shanu ta Potiskum a jihar Yobe

Kasuwar Fatiskum a jihar Yobe: Wannan kasuwa na da girman gaske, ta kuma yi suna a wajen cinikin Shanu da ake fidda da su zuwa wasu wurare a ciki da kuma wajen kasar nan, duk da rikicin Boko Haram. Za a ka iya samun rahusa a farashin shanu a wannan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng