"Za a Iya Ƙarar da Ƴan Bindiga a Mako 2," Gwamna Ya Tona Halayen Ƴan Sanda da Sojoji

"Za a Iya Ƙarar da Ƴan Bindiga a Mako 2," Gwamna Ya Tona Halayen Ƴan Sanda da Sojoji

  • Gwamnan Zamfara ya nuna damuwa kan yadda sojoji da ƴan sanda suka sa wasa a lamarin yaƙi da ƴan bindiga a Arewa maso Yamma
  • Dauda Lawal ya ce halayyar jami'an tsaron waɗanda ke karkashin gwamnatin tarayya ne ya sa shi kafa rundunar asakarawan Zamfara
  • Ya ce a mako biyu za a iya kakkaɓe gaba ɗaya ƴan bindiga idan har da manufar hakan a siyasance to amma ba haka lamarin yake ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya koka kan yadda ƴan sanda da sojoji suka sanya sakaci a yaƙi da ƴan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma.

Gwamma Lawal ya ce halayen da jami'an tsaron gwamnatin tarayya ke nunawa ne ya jawo kirkiro rundunar ƴan sa'kai waɗanda aka fi sani da askarawan Zamfara.

Kara karanta wannan

"Yan bindiga sun shiga uku," Gwamna ya sha alwashin dawo da zaman lafiya duk runtsi

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Gwamna Lawal ya koka kan halayyar jami'an yan saɓda da sojoji a yaƙi da ƴan bindiga Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Ya ce gwamnoni ba su da iko kan jami'an sojoji, ƴan sanda da jami'an tsaron fararen hula na NSCDC, wanda hakan yana kawo masu cikas a ƙoƙarin magance matsalar tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dauda: "Gwamna bai da iko kan sojoji"

Da yake jawabi a cikin shirin Sunrise Daily na Channels tv ranar Talata, Gwamna Lawal ya ce:

"Mu a matsayinmu na gwamnoni, ba mu da iko a kan sojoji, ba mu da iko a kan ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya, shiyasa galibi abin ke sa mu damuwa.
"Za ka ga a lokacin da muke bukatar waɗannan dakarun tsaro ba za a same su ba, bisa haka ne muka ga mafita kawai mu kafa rundunarmu ta kanmu.

Gwamna ya ce jami'an tsaro sun sa sakaci

Gwamnan ya bayyana cewa za a iya magance ƴan bindiga, waɗanda suka mayar da garkuwa da mutane sana'a, cikin makonni biyu idan aka yi niyyar hakan.

Kara karanta wannan

Gwamna ya nuna adawa da kafa 'yan sandan jihohi, ya fadi dalilansa

"A mako biyu za su zama tarihi amma ba a shirya hakan ba a siyasance, mun san su waye ƴan bindigar nan kuma mun san wurin da suke rayuwa."

- Dauda Lawal

Zaman 'yan siyasar Zamfara da 'yan bindiga

Lawal ya yi zargin cewa wasu abokan hamayyarsa na siyasa suna tattaunawa da ‘yan bindiga ba da saninsa ba, Sahara Reporters ta tattaro wannan.

Lokacin da aka tambaye shi ko ya san ainihin wadanda ke tattaunawa da 'yan fashin dajin, sai ya ce, "Duk abin da suke yi mun sani."

Boko Haram sun sace matafiya a titin Maiduguri-Kano

A wani rahoton kuma 'yan Boko Haram sun kai farmaki kan matafiya a babban titin Maiduguri zuwa Kano da yammacin ranar Litinin, 10 ga watan Yuni.

Rahotanni sun ce maharan sun toshe bangare ɗaya na titin da ƙarfe 5:50 na yamma, sun tafi da fasinjoji da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262