Sallah: Bayan Dikko Radda Na Katsina, Gwamnan Sokoto Ya Yi Abin Alkairi ga Ma'aikata

Sallah: Bayan Dikko Radda Na Katsina, Gwamnan Sokoto Ya Yi Abin Alkairi ga Ma'aikata

  • Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bukukuwan sallah babba, ma'aikatan jihar Sokoto za su samu sauki bayan alfarmar gwamna
  • Gwamna Ahmed Aliyu na jihar ya amince da biyan albashin ma'aikata na watan Yuni daga gobe Litinin 10 ga watan Yuni
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Katsina ya ba ma'aikata kyautar N15,000 da kuma bashin N30,0000 saboda bikin sallah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya amince da biyan ma'aikata albashin watan Yuni daga gobe Litinin 10 ga watan Yuni.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin ragewa ma'aikata radadi da kuma yin Sallah cikin walwala.

Kara karanta wannan

"Ku rage albashinku ku biya mu"; Ma'aikata sun fusata kan martanin gwamnoni

Gwamnan Sokoto zai yi abun alheri ga ma'aikatan jihar
Gwamna Ahmed Aliyu zai biya albashi saboda bikin salla a Sokoto. Hoto: Ahmed Aliyu.
Asali: Twitter

Sallah: Ma'aikata za su caba a Sokoto

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Abubakar Bawa ya fitar a yau Lahadi 9 ga watan Yuni, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bawa ya ce biyan zai shafi duka ma'aikatan jihar Sokoto da na kananan hukumomi da kuma ƴan fansho.

Daga bisani gwamnan ya taya al'ummar Musulmai murnan shirye-shiryen gudanar da bukukuwan sallah cikin kwanciyar hankali, cewar Punch.

Yadda ake biyan ma'aikata a Sokoto

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan na biyan albashi ranar 20 zuwa 21 ga kowane wata bayan hawa karagar mulkin jihar.

"Biyan kudin zai shafi duka ma'aikatan jihar Sokoto da na ƙananan hukumomi da kuma ma'aikatan LEA."
"Sannan fara biyan albashin zai shafi hatta ƴan fansho da ke jihar."

- Bawa

Sallah: Radda zai gwangwaje ma'aikata a Katsina

Kara karanta wannan

Katsina: Gwamna ya ba ma’aikata goron sallah N45,000, ya gindaya sharuda

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Umaru Dikko Radda na jihar Katsina ya gwangwaje ma’aikata da barka da sallah a jihar.

Radda ya ba da kyautar N15,000 ga duka ma’aikatan jihar yayin da kuma ya ba su bashin N30,000 domin gudanar da salla cikin walwala ba tare da damuwa ba.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X a jiya Asabar 8 ga watan Yunin da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel