“Ku Rage Albashinku Ku Biya Mu”; Ma’aikata Sun Fusata Kan Martanin Gwamnoni

“Ku Rage Albashinku Ku Biya Mu”; Ma’aikata Sun Fusata Kan Martanin Gwamnoni

  • Ma'aikata a Najeriya sun koka kan matsayar gwamnonin jihohi kan mafi karancin albashi da ake tababa
  • Ma'aikatan sun bukaci gwamnonin su rage albashinsu da alawus domin daukar nauyin biyan albashin
  • Legit Hausa ta ji martanin wasu ma'aikata a jihar Gombe kan matakin da gwamnonin suka ɗauka a ƙasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ma'aikata da dama a Najeriya sun bukaci gwamnonin jihohi su rage albashinsu da alawus domin biyansu hakkokinsu.

Ma'aikatan sun kuma roki gwamnonin su rage alwaus na mukaransu domin biyansu mafi karancin albashin N62,000 da Bola Tinubu ya fitar.

Ma'aikata sun kalubalanci gwamnoni kan mafi karancin albashi
Ma'aikata sun tura bukata ga gwamnoni kan karin albashi. Hoto: @hope_uzodinma1.
Asali: Twitter

Albashi: Martanin wasu ma'aikata a Najeriya

Wasu daga cikin ma'aikatan da suka bukaci boye sunansu sun bayyana Daily Trust cewa abin takaici ne yadda gwamnonin suka yi tirjiya.

Kara karanta wannan

A ina gwamnan Edo ya ga N70,000 na mafi karancin albashi? Shehu ya taso gwamnoni a gaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun tabbatar da daukar matakin shari'a kan gwamnonin idan har ba su fara biyan mafi karancin albashin ba bayan Tinubu ya tabbatar da ita.

"Ba mu ji dadin yadda gwamnoni suka ki amincewa da N60,000 ba ganin yadda suke samun kuɗi sosai daga Gwamnatin Tarayya yanzu."

- Cewar ma'aikataci a Kaduna

Wani ma'aikaci a Bauchi ya bayyana cewa:

"Yawan kudin da Gwamnatin Tarayya ke ba jihohi a kowane wata ya karu amma ba a san inda kudin ke tafiya ba."
"Gwamnanmu ya manta da halin da ma'aikata ke ciki inda ya ke siyan manyan motoci da mukarrabansa da kuma ƴan Majalisun jihar."

Usman Garba da ke jihar Adamawa ya ce:

"Abin takaici ne gwamna ya ce ba zai iya biyan N60,000 ba, ya kamata su rage albashinsu domin biyan ma'aikata mafi karancin albashi."

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: 'Yan Najeriya sun gano tushen matsalolin kasa, sun ambaci suna

Tattaunawar Legit Hausa da wasu ma'aikata

Legit Hausa ta ji martanin wasu ma'aikata a jihar Gombe kan matakin da gwamnonin suka ɗauka.

A'isha Muhammad da ke karamar hukumar Yamaltu Deba ta ce daman babbar matsalar da za a samu daga gwamnoni ne.

"Lokuta da dama gwamnoni ke kawo matsala a mafi karancin albashi har ma da wasu abubuwa na more rayuwa."

Aliyu Muhammad a ma'aikatar lafiya da ke jihar ya ce ya kamata gwamnoni su duba halin da ake ciki domin ragewa ma'aikata radadin da suke ciki a yanzu.

"N62,000 ma ba wani abu ba ne duba da halin da ake ciki saboda tsadar rayuwa amma a hakan gwamnoni suna korafi, ban san mene damuwar ba."

- Aliyu Muhammad

Gwamnoni sun fadi matsayarsu kan karin albashi

Kun ji cewa gwmanonin Najeriya 36 sun yi zama kan mafi karancin albashi inda suka bayyana matsayarsu.

Gwamnonin sun tabbatar da cewa ba za su iya biyan N60,000 ba a matsayin mafi karancin albashi a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel