Gwamnatin Tarayya Za Ta Karawa Ma’aikatan Lafiya Albashi, Ministan Tinubu Ya Yi Bayani
- Gwamnatin tarayya ta dauki matakai domin gyara fannin kiwon lafiya da kuma dawo da ma'aikatan lafiya da suka tafi Turai neman kudi
- Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ya ce gwamnati za ta karawa ma'aikatan lafiya Najeriya albashi nan ba da dadewa ba
- A zantawar mu da wani Dakta Shamsu Abubakar daga jihar Katsina, ya roki likitoci da su hakura da tafiya kasashen ketare neman aiki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ya yi albishir ga likitocin Najeriya, inda ya ce gwamnati za ta kara musu albashi nan ba da dadewa ba.
Da aka tambaye shi ko ma'aikatan lafiya za su samu karin albashi mai tsoka, Ali Pate ya ce nan gaba kadan ma'aikata za su ji labarin karin albashin daga gwamnati.
Likitoci sun yi korafin karancin albashi
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wani shiri na musamman a gidan talabijin Channels kan bikin cikar shugaban kasa Bola Tinubu shekara daya a mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A tsawon shekaru, kwararru a fannin kiwon lafiya a Najeriya sun yi ta korafin karancin albashi da kuma rashin biyan su alawus alawus da sauransu.
Sakamakon rashin samun albashi mai tsoka, wasu da dama daga cikin ma'aikatan lafiya sun yi kaura zuwa ketare, lamarin da ya haifar da karancin likitoci a Najeriya.
"Kokarin gwamnati a kiwon lafiya" - Pate
Da yake magana game da matsalar fannin kiwon lafiya, ministan lafiya ya ce gwamnatin Tinubu ta dauki wasu muhimman matakai na magance wadannan matsalolin.
Sakamakon aiwatar da wadannan matakan, ministan ya ce wasu kwararrun ma'aikatan da suka bar Najeriya zuwa Turai a yanzu suna kokarin dawowa kasar.
Ali Pate ya ce gwamnati ta dauki ma'aikatan jiya, ungozoma da likitoci 2,497 aiki tare da tura su zuwa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a cikin shekara daya.
Kalli tattaunawar a nan kasa:
An roki likitoci su daina tafiya ketare
Wani likita, Shamsu Abubakar daga jihar Katsina, a zantawarsa da Legit Hausa ya koka kan yadda gwamnatocin tarayya da na jihohi ke biris da bukatun ma'aikatan jinya.
Dakta Abubakar ya ce akwai asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da ke bukatar ƙarin likitoci amma hakan ya ki samuwa.
A cewar likitan, akwai bukatar gwamnatocin su rika fifita walwalar likitoci domin cimma burin su na samar da kiwon lafiya mai dorewa a kasar.
Dakta Abubakar ya kuma roki 'yan uwansa likitoci da su hakura da tafiya kasashen waje neman aiki, inda ya ce su zauna gida domin raya asibitocin da suka koyi aiki a ciki.
Rashin lafiya: 'Dan Najeriya ya mutu a Saudiya
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani alhajin Najeriya daga jihar Kebbi, Muhammad Suleman ya rasu bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a kasar Saudiya.
Marigayin na daga cikin maniyyatan Najeriya da suka je Saudiya domin sauke farali a aikin Hajji na bana, kuma an gudanar da jana'izarsa tare da binne shi a Makkah.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng