Aikin Hajji: Najeriya Na Shirin Kafa Asibitoci a Makkah, Ta Na Jiran Amincewar Saudiyya

Aikin Hajji: Najeriya Na Shirin Kafa Asibitoci a Makkah, Ta Na Jiran Amincewar Saudiyya

  • Hukumar alhazai ta kasa ta shawarci maniyyatan Najeriya masu bukatar kulawar lafiya da su ziyarci asibitocin gwamnatin Saudiyya
  • NAHCON ta ce tana jiran amincewar Saudiya domin kafa asibitocinta a Makkah, yayin da ta samu izinin yin hakan a garin Madinah
  • Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Usara ta bayyana hakan a ranar Laraba inda ta gargadi alhazai kan shan magani barkatai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta ce ta na jiran amincewar Saudiya domin kafa asibitoci da za su zama karkashin kulawar likitocin Najeriya da aka tura Makkah.

NAHCON ta yi magana kan kafa asibitoci a Makkah
NAHCON ta nemi amincewar Saudiya domin kafa asibitoci a Makkah. Hoto: @nigeriahajjcom
Asali: Facebook

Najeriya na son kafa asibitoci a Saudiyya

Hukumar ta kuma shawarci maniyyatan Najeriya da ke Makkah domin gudanar da aikin hajjin 2024 da su nemi lafiya a asibitocin kasar Saudiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya za ta karawa ma'aikatan lafiya albashi, ministan Tinubu ya yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Usara ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Yayin da take tabbatar wa alhazai cewa asibitocin Najeriya da ke Makkah na da ma’aikata da kayan aiki, Usara ta ce asibitocin ba za su iya yin aiki ba har sai Saudiya ta ba da izini.

Kiwon lafiya: An ba alhazai shawara

Fatima Usara ta kara da cewa har yanzu babu wata kasa da ke halartar aikin hajjin da aka ba wa izinin kafa asibitoci a Makkah.

Ta kuma shawarci alhazai da su guji shan magani ba bisa ka'ida ba, sannan ta ja hankalin alhazan da su nemi taimako daga kungiyar likitocin Najeriya.

Jaridar Tribune ta ruwaito shugaban kwamitin likitocin NAHCON da aka tura Saudiya, Dr Abubakar Adamu Ismail ya ce an ba Najeriya damar kafa asibitoci a birnin Madinah ban da Makkah.

Kara karanta wannan

Guzirin sigari ko goro: NAHCON ta gargadi alhazan Najeriya masu shirin tafiya Saudiya

Alhajin Najeriya ya rasu a Saudiyya

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da rasuwar daya daga cikin maniyyatan jihar da suka je Saudiya domin gudanar da ayyukan hajjin bana.

Rasuwar Muhammad Sulaiman, ta kara adadin yawan alhazan jihar Kebbi da suka rasu a Makkah zuwa biyu, bayan mutuwar Hajiya Tawakaltu Alako.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel