Cin Zarafin Naira: EFCC Ta Kama Matashi Saboda Likin Kudi a Gidan Rawa

Cin Zarafin Naira: EFCC Ta Kama Matashi Saboda Likin Kudi a Gidan Rawa

  • Hukuma mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta cafke wani matashi bisa zarginsa da cin zarafin Naira
  • EFCC ta ce ana zargin matashin ya yi amfani da takardun kudin N200 wajen yin manni a wani gidan rawa a jihar Gombe
  • Bayan kama matashin da ake zargin, hukumar EFCC ta bayyana matakin da za ta ɗauka domin ya zama darasi ga ƴan baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Hukuma mai yaki da yiwa tattalin kasa zagon kasa (EFCC) ta sanar da kama wani matashi a jihar Gombe bisa zargin cin zarafin Naira.

Manna kudi
EFCC ta kama matashi bisa cin zarafin Naira a Gombe. Hoto: @bashirahmaad|@officialEFCC
Asali: Twitter

A yau Laraba ne hukumar EFCC ta wallafa labarin a shafinta na X inda ta ce jami'anta a jihar Gombe sun kama matashin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kinkimo namijin aikin da zai amfani mutane miliyan 30 a Najeriya

Matashin mai suna Zachariyya Muhammad ya amsa laifinsa yayin da hukumar ta ke yi masa tambayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda EFFC ta gano matashin a bidiyo

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta samu bidiyon matashin ne yana rawa yana manna kudi 'yan N200 a wani gidan rawa da ke Tufure a jihar Gombe.

Bayan tsananta bincike, hukumar ta samo matashin, da aka nuna masa bidiyon sai ya tabbatar da cewa shi ne ya aikata laifin.

Matakin da EFCC ta dauka kan matashin

Hukumar ta ce a halin yanzu za ta mika Zachariyya Muhammad gaban kotu domin Alkali ya bincikesa da kuma yanke masa hukuncin da ya dace.

Kama Zachariyya Muhammad ya biyo bayan cafke shahararrun mutane da hukumar ta yi a kwanan nan domin yaki da cin zarafi Naira.

Kara karanta wannan

Shahararren malamin Kano ya yi magana bayan an tashi da sarakuna 2 a gari

An bukaci EFCC ta kama dan takara

A wani rahoton, kun ji cewa gamayyar kungiyoyin fararen hula karkashin kungiyar NCSO sun nemi hukumar EFCC da ta kama tare da hukunta Monday Okpebolo.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar NCSO, ta zargi Okpebolo, wanda shi ne dan takarar gwamnan jihar Edo da cin zarafin Naira a wani taron biki.

An ce cin zarafin Naira ya sabawa dokar babban bankin Najeriya (CBN) ta 2007 wanda ka iya kaiwa ga daure mutum wata shida a gidan gyaran hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel