Kwana dubu na barawo, kwana daya na mai kaya: an kama barayin Awaki a Gombe (Hotuna)

Kwana dubu na barawo, kwana daya na mai kaya: an kama barayin Awaki a Gombe (Hotuna)

Dubun wasu barayin awaki ta cika a ranar Juma’a, 8 ga watan Yuni a jihar Gombe, bayan kwashe tsawo lokaci suna tafka wannan aikin sibarnabayye, kamar yadda jridar Rariya ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’an hukumar Gombe Marshal ne suka samu nasarar cafke wadannan barayi a kasuwar awaki na Tumfure da karamar hukumar Akko na jihar Gombe.

KU KARANTA: Wata daliba a jihar Sakkwato ta kashe jaririnta dan gaba da fatiha

Kwana dubu na barawo, kwana daya na mai kaya: an kama barayin Awaki a Gombe (Hotuna)
Barayin

Zuwa yanzu hukumar Marshal a karkashin jagorancin shugaban ayyuka na hukumar, D.J Maitaya, ta mika barayin ga jami’an hukumar SARS don cigaba da gudanar da bincike.

Sai dai wani abu makamacin wannan ya faru a kwanakin baya, inda hukumar EFCC ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan a matsayin wanda ake tuhuma da cin makudan kudaden gwamnati, wanda hakan ya tayar da kura, inda har Sheikh Gumi ke goyon bayansu.

Kwana dubu na barawo, kwana daya na mai kaya: an kama barayin Awaki a Gombe (Hotuna)
Barayin

Don haka tambayar anan shine shin su barayin nan basu da galihu ne su da aka yi musu wannan wulakancin? Ko kuwa don su ba sanannun mutane bane? Ko kuwa satar awaki ya fi satar kudin al’umma.?

Kwana dubu na barawo, kwana daya na mai kaya: an kama barayin Awaki a Gombe (Hotuna)
Barayin

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel