An Dauki Mataki da 'Yan Sanda Suka Kama Sojoji, Jami'ai da Laifin Fashi da Makami

An Dauki Mataki da 'Yan Sanda Suka Kama Sojoji, Jami'ai da Laifin Fashi da Makami

  • Rundunar yan sanda a jihar Ribas ta tabbatar da kama yan fashi da makami da ake zargi da karkatar da motar abinci
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da cewa cikin mutanen da aka kama akwai jami'an soji da na NSCDC
  • Har ila yau, kakakin ta bayyana wa manema labarai hukuncin da rundunar soji ta dauka kan jami'anta da aka kama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Rundunar yan sanda a jihar Ribas ta tabbatar da kama yan fashi da makami da ake zargi da aikata manyan laifuffuka.

sojoiji
An kori sojoji bisa laifin fashi da makami. Hoto Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutane 13 rundunar yan sanda ta kama ciki har da jami'an tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda a Katsina sun musanta kisan mutane 40, sun fadi adadin da aka rasa

Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Ribas ce, Grace Iringe-Koko ta sanar da lamarin a jiya Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan sanda suka kama 'yan fashi

Kakakin rundunar yan sandar ta bayyana cewa sun fara bincike ne biyo bayan sata da aka yi a wani gida.

A cewar kakakin, rundunar yan sanda sun kama mutane biyu a sanadiyyar satar kuma hakan ne ya sa suka tsananta bincike har suka kama sauran barayin.

Jami'an tsaron da 'yan sanda suka kama

A bayanin da rundunar yan sandan jihar ta yi, an kama jami'an soji hudu da jami'in NSCDC daya da hannu a laifin fashi da makami.

An kama jami'an ne bisa karkatar da babbar mota dauke da abinci, takin zamani, kayan sawa da sauran abubuwa da dama.

Wani matakin rundunar soji ta dauka?

Jami'an tsaron da ake zargi sun tabbatar da aikata laifin barin wuraren ayyukansu da shiga ayyukan ta'addanci, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka dalibai 2 da suka sace a Jami'a, ƴan sanda sun magantu

Saboda haka rundunar sojin Najeriya ta kori jami'an nata tare da mika su ga rundunar yan sanda domin musu hukuncin da ya dace.

Rundunar soji ta kori jami'anta a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta sanar da korar sojoji biyu da ta kama da laifin sata a matatar man Dangote a jihar Legas.

Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ta ce hukuncin ya biyo bayan zurfafa bincike ne a kan wadanda ake zargin da kuma ba su damar kare kansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel