'Yan Sanda a Katsina sun Musanta Kisan Mutane 40, Sun Fadi Adadin da aka Rasa

'Yan Sanda a Katsina sun Musanta Kisan Mutane 40, Sun Fadi Adadin da aka Rasa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun farmaki unguwar Lamido dake karamar hukumar Bakori
  • An samu rahotannin cewa 'yan ta'addar sun kashe akalla mutane 40, amma rundunar yan sandan jihar ta musanta adadin da ake wallafawa
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ta cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa mutane 11 ne suka mutu a harin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina-Rundunar ‘yan sandan Katsina ta musanta labarin cewa 'yan ta'addan da suka kai hari jihar sun kashe mutane 40 a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kara samun nasara, sun ragargaza 'yan ta'adda a Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa mutane 40 ne suka mutu a harin da miyagun suka kai unguwar Lamido a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Rundunar 'yan sanda
'Yan ta'adda sun kashe mutane 11 a jihar Katsina Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa a sanarwar da jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, ya tabbatar da harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun dakile harin 'yan ta'adda

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa wasu ’yan ta’adda dauke da mugayen makamai sun kai hari Unguwar Lamido, kuma sun harbe mutane 11.

Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Peoples Gazette Nigeria ta wallafa cewa ofishin DPO na babban ofishin ’yan sanda a karamar hukumar Bakori ne ya jagoranci jami’ansa da hadin gwiwar ’yan banga suka kai dauki tare da dakile karuwar barnar.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin Najeriya ta fatattaki 'yan ta'adda, an kamo miyagu a Abuja da Oyo

'Labarin karya na yada tsoro,' ASP Aliyu

Kakakin rundunar 'yan sandan ya tabbatarwa Legit Hausa cewa sun yi kokari wajen fatattakar tsagerun, inda ya shawarci jama'a su guji yada labarin kanzon kurege.

ASP Aliyu ya ce yada labarai marasa tushe kan jefa fargaba cikin zukatan al'umma, wanda hakan ba abin so ba ne.

'Yan sanda sun yi galaba kan miyagu

A baya mun kawo muku rahoton cewa sun yi galaba kan 'yan ta'addar da suka sace 'ya'yan 'dan majalisa a jihar Zamfara, Aminu Ardo.

Dakarun 'yan sanda da hadin gwiwar ofishin mai ba shugaban kasa shawara ne suka samu nasarar kubutar da yaran biyu bayan watanni 17.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel