Cakwakiyar da Aka Sani Game da Alkalin da Ya Dakatar da Nada Sabon Sarkin Kano

Cakwakiyar da Aka Sani Game da Alkalin da Ya Dakatar da Nada Sabon Sarkin Kano

Alkalin babbar kotun tarayya da ke Kano, Mai shari’a Abdullahi Mohammed Liman ne ya bayar da umarni na hana gwamnatin jihar Kano mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wannan kuwa daya ne daga cikin cakwakiyan da Alkali Abdullahi Mohammed Liman ya tsinci kansa a ciki, wanda a yanzu suka bayyana a fili.

Mai shari’a Liman, mai shekaru 65, ya kasance alkali tun a ranar 28 ga Yuli, 2000. Alkalin da aka daga darajarsa zuwa kotun daukaka kara ya fito ne daga jihar Nasarawa.

Abin da muka sani game da Mai shari'a Abdullahi Liman
Cakwakiya 7 da Mai shari'a A.M Liman ya jefa kansa kafin hana nada sarki a Kano. Hoto: Jaafar, Jaafar, Ado Bayero II, sanusilamidoofficial
Asali: Facebook

A cikin wannan labarin, shugaban sashen shari’a na jaridar Daily Trust, John Chuks Azu, ya yi tsokaci kan kalubale bakwai da Mai shari’a Liman ya fuskanta.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Kamar Sanusi II, shi ma Aminu Bayero ya yi zaman fada a Nassarawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Umarnin dakatar da nadin Sanusi II

A ranar 24 ga watan Mayu, Mai shari’a Liman ya bayar da umarnin hana Gwamna Abba Yusuf aiwatar da dokar da ta soke masarautun Kano ta shekarar 2019 wadda za ta mayar da Sarki Sanusi II kan kujerarsa.

Umarnin ya biyo bayan karar da Sarkin Dawaki na Masarautar Kano, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar.

Wannan umarni dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a kan wanda zai zauna kan kujerar sarki tsakanin Sarki Sanusi II da tsohon Sarki Aminu Ado Bayero.

Ana kan tafka muhawara kan ko kotu na da hurumin sauraron wannan karar kasancewar batun sarauta na jiha, wanda manyan kotunan jihohi kawai ke sauraren su.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa ana zargin an yi amfani da sa hannun boge na alkalin wajen fitar da wannan takardar.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Ganduje: Tsofaffin gwamnoni da suka fadi zaɓe bayan faɗa da sarakuna

A hannu daya kuma, Gwamna Abba Yusuf ya sha alwashin kai karar alkalin saboda yanke hukunci a lokacin da yake kasar Amurka.

2. Ana zargin Alkalin da rashin da'a

A ranar 16 ga watan Mayu ne hukumar shari’a ta kasa (NJC) ta sanar da karin girma ga alkalai 22 zuwa kotun daukaka kara ciki har da Mai shari’a A. M Liman.

Majalisar ta kara masa girma ne bayan ta yi watsi da karar da aka shigar kan Mai shari’a Liman da wasu alkalai 34 bisa zargin rashin da’a a aiki, in ji rahoton Vanguard.

3. Kawo tsaiko a dakatar da Ganduje

Mai shari’a Liman ya bayar da umarni a ranar 18 ga Afrilu na hana a dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje.

Wannan umarnin ya jawo ce-ce-ku-ce saboda ya fitar da shi ne duk da umarnin da wata babbar kotu ta bayar a baya wanda ya tabbatar da dakatarwar.

Kara karanta wannan

Rikicin sarautar Kano: Ɗan Sarki Sanusi II, Ashraf ya yi shaguɓe ga Aminu Ado Bayero

Wani bangare na jam’iyyar ya shigar da karar dakatarwar ne saboda zargin karbar rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Kano.

4. Alkalin da ya hana kama Ganduje

Mai shari’a Liman a ranar 8 ga Yuli, 2023, ya hana hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano tuhuma, kamawa, gayyata ko tsare Ganduje.

Umurnin ya biyo bayan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na yin bincike kan wani bidiyo na 2018 da ake zargin Ganduje yana karbar makudan kudi daga hannun wani dan kwangila.

5. 'Dan takara ya zargi Alkali Liman

A shekarar 2022, dan takarar jam'iyyar NCP a zaben gwamnan jihar Edo na 2020, Peters Osawaru Omoragbon, ya zargi Mai shari'a Liman a bainar jama'a da "rashin da'a."

A watan Mayun 2020 ne Omoragbon ya shigar da kara a gaban kotun Liman da ke jihar Edo kan hukumar INEC, inda ya ce zai yanke hukunci a watan Disamba na shekarar amma har bayan shekara bai yi hakan ba.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya bayyana rawar da Tinubu ya taka wajen dawo da shi kan sarautar Kano

Omoragbon ya fitar da wata sanarwa inda ya zargi Mai shari’a Liman da yin watsi da shari’ar da take yi wa INEC kan zaben gwamnan jihar Edo.

6. DSS ta kama alkalai a 2016

Mai shari’a Liman na cikin alkalan da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kai samame gidajensu bisa zargin karbar cin hanci da rashawa a shekarar 2016.

Jaridar The Cable ta ruwaito gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya hana a kama Liman, amma dai hukumar DSS ta yi zargin cewa ta kwato dala miliyan 2 a gidansa na Fatakwal.

Da yake mayar da martani, alkalin ya ce bai taba ganin irin wannan adadin kudin ba, yana mai yin nuni da zai yi murabus daga aikin idan har ya mallaki wadannan kudi, in ji Daily Post.

7. Shari'ar rashawar N25bn ta Igbinedion

A Afrilun 2015, Mai shari’a Liman da ke jagorantar wata babbar kotu a Edo, ya karbi shari’ar cin hanci da ta hada da Michael Igbinedion, kanin tsohon gwamnan Edo, Lucky Igbinedion.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Muhammadu Sanusi II ya ke maraba da Kanawa a fada duk da halin da ake ciki

Patrick Eboigbodin, wanda mataimaki ne ga tsohon Gwamna Igbinedion, shi ne wanda ake tuhuma tare da Michael Igbinedion a kan zambar Naira biliyan 25, in ji rahoton The Cable.

Ya yanke wa Michael Igbinedion hukunci kan laifuffuka uku cikin 81 da hukumar EFCC ta gabatar, tare da ba shi damar biyan tarar Naira miliyan 3 maimakon zaman yari.

Sai dai mai shari’a Liman ya ki amincewa da ba Eboigbodin zabin biyan tara inda ya yanke masa hukuncin zaman yari na shekaru 20 kan samunsa da laifuffuka 10.

Wannan hukuncin nasa ya jawo an yi alamar tambaya kan dalilin da ya sa ya ba babban wanda ake tuhuma zabin tara amma ya hana dayan wanda ake tuhumar zabin biyan tarar.

Tsohon Sarkin Gaya ya dauki kaddara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon sarkin Gaya da sabuwar dokar masarautun Kano ta tsige shi daga mulki ya ce ya dauki wannan matakin a matsayin 'mukaddari daga Allah.'

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II: Jerin manyan sarakunan Arewa da aka tsige a Najeriya tare da dalilai

Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya kuma ce ba zai kalubalanci matakin a kotu ba kuma idan aka ba shi wani mukamin zai karba da hannu biyu-biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel