Alkalin da Ya Yi Koƙarin Hana Naɗin Sanusi II Ya Jawo Wa Kansa, Gwamna Ya Ɗauki Mataki

Alkalin da Ya Yi Koƙarin Hana Naɗin Sanusi II Ya Jawo Wa Kansa, Gwamna Ya Ɗauki Mataki

  • Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin kai ƙarar alkalin da ya yi yunkurin hana naɗin Sanusi II ga ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF)
  • Gwamnan ya ce umarnin da alkalin babbar kotun tarayya ya bayar cin mutunci ne kuma ba zai bar lamarin da wuce haka kurum ba
  • Alkalin ya umarci gwamnatin Kano ta dakatar da naɗin Sarki Sanusi da kuma rushe masarautu biyar da Abdullahi Ganduje ya ƙirƙiro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sha alwashin ɗaukar mataki kan alƙalin da ya yi kokarin dakatar da naɗin Sarki Muhammadu Sanusi II.

Gwamna ya ce zai kai ƙorafin alkalin gaban kungiyar gwamnonin Najeriya domin abin da ya aikata ba komai bane illa cin mutuncin ɓangaren shari'a.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II ya zama sabon sarkin Kano a hukumance, bidiyo ya fito

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Abba Gida Gida.
Gwamnan Kano zai kai ƙorafin alkalin kotun tarayya gaban NGF Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Abba ya faɗi haka ne yayin da yake mayar da martani ga umarnin kotu, wadda ta ce a dakatar da naɗin Sanusi da sauke sarakuna biyar na Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane umarni alkalin kotun ya bayar?

Kamar yadda Daily Trust ta kawo, Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman na babbar kotun tarayya mai zama a Kano ne ya yanke wannan hukunci.

Alkalin ya umarci sufetan ƴan sanda na ƙasa, kwamishinan ƴan sanda na Kano, hukumar tsaro ta NSCDC da DSS kar su kuskura su bi sabuwar dokar masarautar Kano.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin ne bisa bukatar da Aminu Babba Danagundi wanda ke rike da sarautar Sarkin Dawaki Babba ya gabatar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamna ya faɗi matakin da zai ɗauka

Amma da yake martani jim kaɗan bayan miƙa takardar kama aiki ga Sarki Sanusi II a gidan gwamnati ranar Jumu'a, Gwamna Abba ya ce:

Kara karanta wannan

Ana zargin shi ya shirya komai, Kwankwaso ya yi magana kan tsige sarakunan Kano

"Mutumin da ya bayar da umarnin kotu yana Amurka amma daga can yake ba mu umarni mu daina abin da muke, wannan cin mutunci ne zan kai ƙorafi ƙungiyar gwamnoni domin a ɗauki mataki.
"Muna bin doka sau da kafa shiyasa muka yi abin da muka yi kowa na gani, duk waɗanda ke son tabbatar da doka za su amince da abin da muka yi."

Kwankwaso ya musanta hannu a tsige sarakuna

A wani rahoton kuma jagoran ɗarikar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ba hannunsa a rushe masarautun Kano biyar da Abdullahi Ganduje ya ƙirƙiro.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa duk abubuwan da ke faruwa ba ya cikin jihar Kano amma yana dab da komawa kuma zai nemi ƙarin bayani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel