Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano Ta Mika Kokon Bararta Wajen Shugaba Tinubu
- Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tsakani kan rikicin da ke faruwa a masarautar Kano
- Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo, shi ne ya yi wannan kiran ga shugaban ƙasan domin hana jihar faɗawa cikin rikici
- Mataimakin gwamnan ya kuma kare matakin gwamnatin jihar na dawo da Muhammadu Sanusi II kan sarautar Kano inda ya ce ta bi hanyar da ta dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya sa baki a rikicin masarautar Kano.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yi wannan kiran yayin ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar ranar Litinin.
Kano: Ana so Tinubu ya sa baki
Mataimakin gwamnan ya ce shiga tsakanin na Bola Tinubu zai ceto jihar daga faɗawa cikin rikici, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminu Gwarzo ya ce jihar ta yi suna wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali, duk da sarƙaƙiyar siyasar da take da ita.
Buƙatar gwamnatin Kano wajen Tinubu
Mataimakin gwamnan ya buƙaci shugaban ƙasan da ya dauki matakan da suka dace domin kaucewa ƙara ruruwar wutar rikicin.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta bi tsarin da ya dace wajen mayar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Aminu Gwarzo ya bayyana cewa ba a ba gwamnatin jihar wani umarnin kotu ba dangane da dakatar da naɗin Muhammadu Sanusi II.
Mataimakin gwamnan ya ce roƙon nasa na da nufin tabbatar da warware rikicin cikin lumana da kuma tabbatar da zaman lafiyar jihar.
Rawar Tinubu wajen dawo da Sanusi II
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bai yi katsalandan ba wajen dawo da shi kan sarautar Kano.
Sabon sarkin na Kano ya ce Tinubu ya fahimci cewa abin da yake faruwa a Kano al'amari ne na cikin gida kuma ya bijirewa duk wani matsin lamba domin ya yi katsalandan a ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng