Sarki 2 a Lokaci 1: Lauyoyin Sun Fitar da Jawabi Ganin An Jibge Jami’an Sojoji

Sarki 2 a Lokaci 1: Lauyoyin Sun Fitar da Jawabi Ganin An Jibge Jami’an Sojoji

  • Kungiyar Lauyoyi watau NBA ta reshen Kano ta fito ta yi magana ganin an samu Sarakuna biyu a Lokaci guda
  • Shugaban NBA, Sagir Gezawa ya ce idan an sabawa umarnin kotu, ba dakarun sojoji za a jibgwa mutanen Kano ba
  • Lauyan ya soki matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a matsayin martani kan maido Muhammadu Sanusi II

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Kungiyar NBA ta lauyoyi ta reshen jihar Kano ta yi Allah-wadai da yadda aka shigo da jami’an tsaro a rikicin masarauta.

Kungiyar lauyoyin na Kano suna ganin wannan yunkuri da sunan neman tabbatar da hukuncin kotun tarayya ya sabawa doka.

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf ya bijirewa kotu wajen nadin Sarkin Kano Hoto: Kingsley Moghalu/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ana zargin gwamna da bijerewa kotu

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Lauya ya lalubo lungun da Abba ya saba doka wajen maido Sanusi II

Daily Nigerian ta rahoto cewa neman tursasa bin umarnin kotu da taimakon sojoji da ‘yan sanda ba shi ne abin da ya kamata ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar lauyoyin ta fito ne ta bakin shugaban NBA na reshen na Kano, Sagir Gezawa.

Sagir Gezawa ya bayyana cewa akwai hanyoyin doka da ake bi domin tabbatar da cewa an yi biyayya ga hukuncin da alkali ya yi.

"A matsayinmu na lauyoyi, mun damu sosai da abubuwan da suke faruwa ta hanyoyi da-dama kamar:
Majalisar dokoki ta na da hurumin yin doka, kuma da zarar an amince da ita, gwamna yana da hakkin ratabba hannu a dokar.
Da zarar gwamna ya sa hannu, ta zama doka kuma dole wadanda abin ya shafa suyi biyayya kuma dole kotu ta tabbatar da ita."

- Kungiyar NBA

Sanusi II: Matakin da za a dauka kan Abba

Kara karanta wannan

"Babu wanda ya fi ƙarfin doka," Sarkin Kano da aka tsige ya mayar da martani mai zafi

Jawabin ya ce idan ana zargin an sabawa kotu, ba aikin sojoji ba ne aiko dakaru, wannan abin tir ne da ke sa a tuna da mulkin soji.

NBA ta ce doka ta tanadi matakan da ake bi idan an bijirewa kotu, sai an shigar da kara gaban alkali kuma an samu mutum da laifi.

A karshe kungiyar lauyoyin na jihar Kano ta ce dole a tabbatar da zaman lafiya tare da kira ga jami’an tsaro su yi abin da ya dace.

Abba ya ki bin hukuncin Alkali a Kano

Ana da labari wata kotun tarayya ta ba da umarni a dakata da sauke Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan da aka kirkiro a 2019.

Gwamnatin jihar Kano tayi fatali da wannan hukunci, har Abba Kabir Yusuf ya yi barazanar kai karar alkalin a wajen nada sabon sarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel