Sarkin Kano: Duk da Umarnin Kotu, Gwamna Abba Zai Mika Takardar Nadi Ga Sanusi II

Sarkin Kano: Duk da Umarnin Kotu, Gwamna Abba Zai Mika Takardar Nadi Ga Sanusi II

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf zai gabatar da takardar nadi ga mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na 16
  • Za a gudanar da taron mika takardar nadin ne da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Juma'a a dakin taro na fadar gwamnati
  • Wannan kuwa na zuwa ne bayan da babbar kotun tarayya da ke jihar ta umarci gwamnatin jihar da ta dakatar da nada Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta bayyana lokacin da za ta ba Muhammadu Sanusi II takardar nada shi sarautar Sarkin Kano na 16.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai gabatar da takardar nadin ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 16 a Africa House dake fadar gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya dawo gida, ya isa fadar gwamnatin Kano a shirin komawa sarauta

Gwamnatin Kano ta yi magana kan mika takardar nadi ga Sarki Sanusi
Yau Juma'a Gwamna Abba zai ba Sanusi II takardar nada shi Sarkin Kano. Hoto: @masarautarkano
Asali: Original

Mai taimakawa gwamnan Kano na musamman kan kafofin sadarwa na zamani, Abdullahi I. Ibrahim ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta hana nada sabon Sarkin Kano

Wannan kuwa na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar da ta dakatar da nada Sanusi II.

Mun ruwaito Mai shari’a Mohammed Liman ya bayar da wannan umarni ne a cikin karar da Sarkin Dawaki Babba na masarautar Kano, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar.

Alkalin kotun ya kuma umarci gwamnatin jihar da ta dakatar da aiwatar da dokar da majalisar dokokin Kano ta yi na rusa masarautu biyar na jihar.

Gwamna Abba zai ba Sanusi II takarda

Sai dai a wannan sanarwa da Abdullahi I. Ibrahim ya fitar a safiyar Juma'a, ya ce Gwamna Abba zai ba Sanusi II takardar nadin ne da karfe 9:00 na safiyar yau.

Kara karanta wannan

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga mayar da Sanusi II gidan sarauta

Mai taimakawa gwamnan ya ce:

"Da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Gwamna Abba Kabir Yusuf zai gabatar da takardar nadi ga mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a Africa House dake fadar gwamnatin Kano."

"Dalilin nada Sanusi II Sarkin Kano" - Abba

Tun da fari, mun ruwaito Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na daya daga cikin alkawuran da ya daukarwa mutanen Kano.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar da sanarwa kan hakan, inda ya ce gwamnan ya ba sarakunan da aka tsige wa'adin awanni 48 su bar gidajen sarauta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel