APC Ta Samu Karuwa Bayan Manyan Sanatoci Guda 2 Sun Watsar da Jam'iyyarsu da Magoya Bayansu

APC Ta Samu Karuwa Bayan Manyan Sanatoci Guda 2 Sun Watsar da Jam'iyyarsu da Magoya Bayansu

  • Jam'iyyar APC ta sake sabon kamu bayan sanatoci biyu daga jihar Anambra sun sauya sheka zuwa jam'iyyar
  • Daga cikin wadanda su ka sauya shekan akwai Sanata Ifeanyi Ubah da Sanata Uche Ekwunife
  • Shugaban jam'iyyar a jihar, Cif Basil Ejidike da kuma Andy Ubah sun godewa sanatocin da shigowa jam'iyyarsu

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Jam'iyyar APC a jihar Anambra ta karbi sabbin tuba wadanda su ka sauya sheka zuwa jam'iyyar.

Daga cikin wadanda su ka sauya shekan akwai Sanata Ifeanyi Uba da kuma Sanata Uche Ekwunife da magoya bayansu, cewar Punch.

Jam'iyyar APC ta sake kwasar garabasa bayan sanatoci biyu sun koma jam'iyyar
Sanatoci biyu sun sauya sheka zuwa APC a Anambra. Hoto: Abdullahi Ganduje, Ifeanyi Ubah.
Asali: Facebook

Waye ya karbi sabbin tuban zuwa APC?

Wannan shi ne karon farko bayan Ubah ya sauya shekar zai kawo ziyara uwar jam'iyyar da ke Anambra, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno PDP yayin da Atiku da fitaccen gwamna suke neman iko, karin bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam'iyyar a jihar, Cif Basil Ejidike da kuma Andy Ubah sun godewa sanatocin da shigowa jam'iyyarsu.

Ejidike wanda a hukumance ya karbi sabbin tuban ya godewa Shugaba Tinubu kan yadda ya ke gudanar da shugabancinsa.

Ya kuma roki sauran 'yan jam'iyyar da su ci gaba da bai wa jam'iyyar goyon baya kamar yadda su ka saba.

Wane martani shugaban APC ya yi?

Ya kara da cewa jam'iyyar APC ta shirya kwace jihar a zaben shekarar 2025 inda ya ce su na da karfin gwiwa.

Ya ce:

"Mu na da tabbacin cin nasara a wannan zabe mai zuwa saboda duk abin da ake bukata mun shirya su.
"Shekarar 2025 za ta ba mu damar tsayawa takara da kuma yin nasara a zaben jihar Anambra."

Ejidike ya bukaci 'yan jam'iyyar da su tsaya tsayin daka don tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a zabukan, cewar NewsNow.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama a shari'ar neman tsige gwamna mai ci, ta ba da dalilai

Yayin martaninshi, Sanata Ubah ya ce shigar shi jam'iyyar ya kawo karshen jiran da APC ke yi na kwace kujera a jihar.

APC ta gargadi Abba Kabir kan hukuncin kotu

A wani labarin, Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta gargadi Gwamna Abba Kabir da ya jira hukucin Kotun Koli tukunna.

Jam'iyyar ta zargi gwamnan da hallaka kudaden al'ummar jihar wurin daukar nauyin zanga-zangar da ke gudana a jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli kan shari'ar zaben gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel