“Ka Hakura da Zaman Kano”: Kungiyar Arewa Ta Ba Sarki Aminu Shawara Bayan an Tsige Shi

“Ka Hakura da Zaman Kano”: Kungiyar Arewa Ta Ba Sarki Aminu Shawara Bayan an Tsige Shi

  • Wata kungiyar Arewa ta nemi tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da ya bar jihar domin a samu zaman lafiya
  • Kungiyar ta ce dawowar Sarki Aminu Kano da kafa fada a Nasarawa, wani mataki ne da zai iya kawo tashin hankali a Kano
  • A hannu daya, tsohon Sarkin Kano, Aminu Bayero, ya yu kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da zaman lafiya da bin doka da oda

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Kungiyar 'Arewa Social Contract Initiative' a ranar Lahadi, 26 ga watan Mayu, ta bukaci hambararren sarkin Kano, Aminu Bayero, da ya bar jihar domin a samu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Zanga zanga ta barke a fadar masarautar Gaya da majalisa ta rusa

Kungiyar Arewa ta yi magana kan Sarki Aminu
Kungiyar Arewa ta nemi Sarki Aminu Bayero ya bar Kano. Hoto: @hrh_ado
Asali: Twitter

Sarki Aminu wanda aka tsige shi tare da wasu sarakuna hudu masu daraja ta daya bayan kafa sabuwar doka, ya koma Kano tare da kafa fada a Gidan Nasarawa.

An nemi Sarki Aminu ya bar Kano

Jaridar The Nation ta ruwaito shugaban kungiyar ASCI na kasa, Alhaji Sani Mahmoud Darma ya ce har sai Sarki Aminu ya bar Kano ne za a samu zaman lafiya a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darma, ya bayyana cewa binciken kungiyar ya nuna Sarki Bayero a matsayin wanda ke kara rura wutar rikicin masarautar a don haka "ya kamata ya bar Kano".

Abin da ya kamata Sarki Aminu ya yi

A cewar shugaban kungiyar:

“Abin takaici ne a ce bayan an tube shi daga sarki kuma har ya amince da hukuncin, amma wasu daga sama suka dawo da shi Kano da zummar karbar masa kujerar.

Kara karanta wannan

Rikicin sarautar Kano: Ɗan Sarki Sanusi II, Ashraf ya yi shaguɓe ga Aminu Ado Bayero

“Idan ya ji an tube rawaninsa ba bisa ka’ida ba, to kamata ya yi ya nemi wani gari ya koma can da zama, idan ya so sai ya shigar da kara a kotu domin a bi masa kadinsa.
Amma dawowa Kano da yunkurin mamaye fadar, alama ce da ke nuna cewa yana son kawo tashin hankali da hargitsi a Kano.”

Sarki Aminu ya magantu bayan tsige shi

A hannu daya, jaridar Premium Times ta ruwaito tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya yu kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da zaman lafiya da bin doka da oda.

Tsohon sarkin ya yi wannan kiran ne a jiya Asabar jim kadan bayan karbar kwamishinan ‘yan sandan jihar a wata karamar fadar da ke Nasarawa.

An gudanar da zanga-zanga a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu matasa a karamar hukumar Gaya da ke jihar Kano sun gudanar da zanga-zanga ta nuna adawa da rusa masarautu biyar na jihar.

Masu zanga-zanga sun koka kan yadda gwamnatin Abba Yusuf ta tsige sarakuna biyar na gargajiya da aka samar shekaru biyar da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.