Sarki Muhammadu Sunusi II ya Jagoranci SallarJuma'a a Fadar Gwamnatin Kano

Sarki Muhammadu Sunusi II ya Jagoranci SallarJuma'a a Fadar Gwamnatin Kano

  • Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II ya jagoranci sallar Juma'a a a yau jim kadan bayan karbar sandar mulki da dubban al'umma suka halarta a gidan gwamnati
  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana cewa Sarkin ne zai jagoranci sallah a jawabinsa bayan tabbatar da shi a kan karagarsa shekaru hudu bayan tunbuke shi da tsohuwar gwamnati ta yi
  • Ya bayyana sabon sarkin da cewa yana da ilimin addini da na zamani, sannan ya jaddada cewa bayan sallar ne mai martaba zai koma fadarsa domin ci gaba da gudanar da harkokin mulki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

Jihar Kano-Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya jagoranci sallar Juma'a a masallacin dake fadar gwamnatin Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana cewa sabon sarkin ne zai jagorance su sallah jim kadan bayan tabbatar da shi a matsayin sabon sarkin Kano.

Sarkin Sanusi
Sarkin Kano na 16 Malam Muhammadu Sunusi II ya jagoranci sallar Juma'a Hoto: Malam Muhammadu Sanusi II
Asali: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa gwamnan ya shaidawa dandazon masoyan Sarkin cewa bayan ya idar da salla zai koma fadarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Sarki ya dawo kujerarsa,' Abba Gida-gida

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya umarci dukkanin jami'an gwamnati da suka halarci taron nadin Malam Muhammadu Sunusi II da su tsaya su ji hudubar sabon Sarki.

BBC pidgin ta ruwaito cewa an nada Sarki Muhammadu Sunusi II ne duk da umarnin kotu da ya haramta hakan.

Amma a kalaman Gwamna Abba gida-gida:

"Ai ba sabon Sarki ba ne, dama kujerarsa ce ta dawo bayan ya bar ta na wucin gadi."

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin Sanusi II ya yi kira 1 wajen taya shi murnar dawowa karaga

"Idan Allah Ya yarda idan muka gama wannan taro, masu girma hakimai, masu girma 'yan majalisa, masu girma shugabannin kananan hukumomi da duk wadanda suka dace, ku zauna
"Sarkinmu adali, Sarkinmu mai ilimin addinin musulunci zai zo wannan masallaci na gidan gwamnati zai yi mana huduba, zai jagorance mu sallar Juma'a."

- Abba Kabir Yusuf

A kalamansa, sabon Sarkin Kano ya bayyana sake nada shi sarautar da bukata da addu'ar mutanen Kano da suka yi ba dare ba rana.

An nada sabon sarkin Kano

Mun kawo muku labarin cewa Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya nada Malam Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon sarkin Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya mikawa Malam Sanusi II takardar tabbatar masa da sarautar shekaru hudu bayan tsohuwar gwamnati ta tunbuke shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel