Sarautar Kano: Abubuwa 3 da Suka Ja Hankalin Al’umma Bayan Maida Sarki Sanusi II Kujerarsa

Sarautar Kano: Abubuwa 3 da Suka Ja Hankalin Al’umma Bayan Maida Sarki Sanusi II Kujerarsa

  • A yau Alhamis 23 ga watan Mayu majalisar dokokin Kano ta yi karatu na uku kan rusa dokar da ta kirkiro masarautu biyar a jihar
  • Haka zalika gwaamna Abba ya tabbatar da dawo Muhammadu Sanusi II da tsohuwar gwamnatin jihar ta kora daga sarauta
  • Legit ta tattaro muku manyan abubuwa guda uku da suka ja hankalin al'umma biyo bayan dawo da mai martaba Muhammadu Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A yau Alhamis majilisar dokokin jihar Kano ta rusa masarautu biyar da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.

Sanusi II
Dawo da Muhammadu Sanusi II ya ja hankulan al'ummar Najeriya. Hoto: Sadiq Gentle|Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Facebook

Tuni rusa masarautun ya fara jawo hankulan al'umma a kafafen sadarwa musamman dawowar Muhammadu Sanusi II kujerarsa.

Kara karanta wannan

Abba ya tabbatar da korar Aminu Ado Bayero, ya sanya hannu a dokar da ta rusa su

A wannan rahoton, mun tattaro muku manyan abubuwa da al'umma suka fi mayar da hankali a kai tun bayan da majalisar ta rusa dokar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Cire tuta a fadar Kano

Tun bayan sanarwar da ya fito daga majalisar dokokin jihar Kano, al'ummar duniya suka zuba ido su ga yadda fadar Kano za ta kasance.

A cikin lokaci kankani sai ga an cire tuta a masarautar Kano wanda hakan yake nuna babu sarki a garin.

2. Fitar Sarkin Kano daga fada

Rusa masarautun ya sa mutane na zuba ido kan yadda masu mulkin za su fita daga fada wanda hakan yana haifar da tausayi a fuskokin masoyansu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda mai martaba Aminu Ado Bayero ke shirin fita daga fadar Kano, hakan zai ba Muhammadu Sanusi II damar hawa karagar mulki.

Kara karanta wannan

Dawo-Dawo: An sanar da sabon Sarkin Kano, Sanusi II ya zama sarki a karo na biyu

3. Ziyarar Donald Duke ga Sanusi II

A lokacin da ake shirin sanar da dawowar sarki Muhammadu Sanusi II, Donald Duke ya fara kai masa ziyara domin taya shi murna.

Donald Duke ya kaiwa Muhammadu Sanusi II ziyarar ne a jihar Ribas yayin da sarkin ya halarci wani taro a jihar, rahoton Leadership.

An ba Abba shawara kan masarautu

A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiya ta al’ummar Rano, Kibiya da Bunkure ta aika muhimmin bukata a gaban gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

Kungiyar ta roki Abba Gida Gida da ya yi watsi da duk wani yunkuri na rushe karin masarautu hudu da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kafa a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel