Kano: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau ya Raba Motoci 107 a Mazabarsa

Kano: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau ya Raba Motoci 107 a Mazabarsa

  • Mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin ya raba motocin bas bas 107 ga direbobin da suka fito daga Kano ta Arewa
  • Barau Jibrin wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) na farko ya raba motocin ne a tsarin biya a hankali cikin farashi mai sauki
  • 'Yan kungiyar masu kula da motocin haya na NURTW ne suka mori tagomashin da a ganinsu zai taimaka matuka wajen bunkasa sana'arsu da saukaka sufuri a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano-Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya rabawa 'yan mazabarsa tallafin motocin sufuri 107.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Arewa guda 5 da Bola Tinubu ya ba manyan mukamai a jami'o'i

Sanata Barau, wanda shi ne Mataimakin Shugaban majalisar kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) na farko kuma mukaddashin shugabanta a yanzu ya raba motocin ne ranar Litinin.

Barau I Jibrin
Sanata Barau Jibrin ya bawa direbobin motoci 60 bisa farashi mai sauki Hoto: Barau Jibrin
Asali: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa Sanatan na da yakinin motocin za su taimaka wajen saukaka zirga-zirga ga al'ummar Kano baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barau Jibrin: Direbobi sun karbi motoci

Direbobin kungiyar Kula da Motocin Haya ta NURTW ne suka yi nasarar sayen motoci a tsarin biya a hankali, kuma a farashi mai sauki kamar yadda suka bayyana.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa an raba motocin ne ga wadanda Sanata Barau ke wakilta, wato Kano ta Arewa.

Daya daga mambobin kungiyar, Malam Rabi’u Bichi da ya rabauta da motar ya ce hakan zai taimaka musu sosai.

Ya ce wannan zai saukaka zirga-zirga sosai a mazabar da ma sauran sassan jihar. Sannan ya yaba da yadda Sanatan ke kawo musu ayyukan ci gaba da saukaka rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta sayawa 'yan majalisa motocin alfarma kan N2.6bn

A madadin sauran wadanda suka samu motocin, Malam Rabi'u Bichi ya yiwa Sanata Barau addu'ar ci gaba da alkhairi ga mutanensa.

Barau ya raba motoci 60

A baya mun ba ku labarin cewa mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin ya raba motoci kirar sharon ga 'yan mazabarsa.

Sanatan ya ce ya raba motocin ne ga wadanda rabonsu ya tsaga domin saukaka musu sufuri daga gida zuwa kasuwa ko ofis ko gonakinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel