NDLEA Ta Fara Farautar Miji da Mata Kan Safarar Hodar Iblis Tsakanin Indiya da Najeriya

NDLEA Ta Fara Farautar Miji da Mata Kan Safarar Hodar Iblis Tsakanin Indiya da Najeriya

  • Hukumar NDLEA ta kama mutane hudu da ke aiki a daba daya wadda ake zargin ta na safarar hodar iblis tsakanin Indiya da Najeriya
  • Bayan dogon bincike, hukumar ta gano cewa wani dan Najeriya, Kazeem Owoalade ne ubadan dabar wanda ke zaune a kasar Indiya
  • A halin yanzu dai, hukumar NDLE ta ayyana Owoalade da matarsa Rashidat Ayinke a matsayin wadanda take nema ruwa a jallo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ayyana neman wasu ma’aurata, Kazeem Omogoriola Owoalade da Rashidat Ayinke Owoalade bisa zargin su da fataucin hodar iblis daga kasar Indiya.

NDLE ta kai mamaya dabar masu safarar hodar iblis.
Legas: NDLEA ta fara farautar miji da mata kan jagorantar dabar safarar hodar Iblis daga Indiya. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

NDLEA ta kama masu safarar hodar iblis

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

Hakan ya biyo bayan mamayar da ta kai dabar masu safarar da ke Legas, inda ta kama mutane hudu da kwato mota da wasu gidaje biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, kuma aka wallafa a shafinta na yanar gizo ranar Lahadi.

Babafemi ya ce an kama wasu mambobin dabar guda biyu Imran Taofeek Olalekan da Ishola Isiaka Olalekan a ranar 3 ga Afrilu, 2024.

An kama su ne suna kokarin safarar hodar iblis mai nauyin kilogiram 3.40 a jirgin Qatar da zai je Oman ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed, MMIA Ikeja Legas.

Hukumar NDLE ta gano bakin zaren

A cewar Babafemi, an gano cewa Imran ne aka dorawa alhakin daukar hodar zuwa kasar Oman, yayin Ishola ya dauke shi aikin bisa umarninshugaban dabar.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta mayarwa Amurka $22,000 da wani dan Najeriya ya sata ta yanar gizo

"A yanzu haka bincike ya nuna Alhaji Kazeem Omogoriola Owoalade wanda ya ke amfani da sunan Abdul Qassim Adisa Balogun a takardar izinin zama a Indiya shi ne shugaban wannan dabar,
"Bayan shafe makonni biyar ana sa ido da kuma bin diddigi an kama wani dan dabar, Hamed Abimbola Saheed, wanda ke aiki kai tsaye da uban dabar a ranar Talata 14 ga watan Mayu a unguwar Abule Egba a Legas."

- A cewar sanarwar kakakin hukumar na NDLE.

Hukuncin kisa kan masu safarar kwayoyi

A wani labarin, majalisar dattawa ta zartar da kudurin da zai kafa dokar yanke hukuncin kisa kan wadanda aka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi.

A halin yanzu dai ana jira shugaban kasa Bola Tinubu ya sa hannu kan wannan kudir domin zama doka, duk da wasu na adawa da kudurin wanda ya shafi 'rayuwa da mutuwa'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.