Wani ango mai fataucin miyagun kwayoyi ya shiga hannu wata daya kafin bikinsa

Wani ango mai fataucin miyagun kwayoyi ya shiga hannu wata daya kafin bikinsa

- Da wuya mafarkin Adendu Kingsley mai shirin zama ango ya zama gaskiya bayan hukumar NDLEA ta kama shi

- Jami’an hukumar ne suka kama mai shirin zama angon dauke da haramtaccen sinadari

- Sai dai bai daura laifin abunda ya same shi a kan kowa ba, inda yace lallai yana sane da hatsarin da ke tattare da hakan a lokacin da zai yi tafiyar

Hukumar hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi watau NDLEA, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja ta kama wani ango da ke shirin aurensa.

Lamarin ya shafi Elechi Adendu Kingsley, wani dan Najeriya mai shekaru 39 wanda aka kama da wata jakar leda a yayin tantancewa a jirgin Habasha mai lamba Et 911., PR News ta ruwaito.

Kinsley, dan asalin karamar hukumar Umulolo da ke jihar Imo wanda ke zama a Brazil tsawon fiye da shekaru 13 da suka gabata yace ba zai daura laifin kama shi da aka yi akan kowa ba.

Wani ango mai fataucin hodar iblis ya shiga hannu wata daya kafin bikinsa
Wani ango mai fataucin hodar iblis ya shiga hannu wata daya kafin bikinsa Hoto: PR News
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Ta tabbata: Ranar Lahadi za a ɗaura auren ango Isah da amarya Janine a Kano

“Ni ba yaro bane kuma na san abunda na sanya kaina a ciki. Na yarda cewa wani ne ya bani amma ni na bukaci cewa zan dauka.” In ji shi.

Kingsley ya ce an yi masa alkawarin naira miliyan 3 da zaran ya kai kwayoyin ga wani mutum a Najeriya lafiya.

KU KARANTA KUMA: Matar Alaramma Abubakar ta haifi ‘yan 3 yan kwanaki bayan an yi garkuwa da mijin nata

Ya zo Najeriya ne domin shirye shiryen aurensa da za a yi a watan Janairun 2021.

Da yake magana a kan wannan sabbin dabaru na fataucin kwayoyi, Kabir Sani Tsakuwa, kwamandan NDLEA filin jirgin saman Abuja, yace tunanin masu fataucin miyagun kwayoyi ya zarta yadda ake zato.

“Abunda ake so damu shine kada mu tsaya a inda tunaninsu yake illa kawai mu dunga zartasu a tunani. Kamar yadda kuka gani, duk wani yunkuri da suka yi, muna sama da su, ga sakamakon hakan muna gani. Ina musu alkawarin sai na birkita tunaninsu.”

A wani labarin, wani direban mota ya basga wa jami'in LASTMA tabarya a kai a ranar Talata, 8 ga watan Disamba.

Hakan ya faru saboda jami'in ya dakatar da direban a kan karya dokar tuki wuraren Jakande a Lekki.

Tuni aka garzaya da direban ofishin 'yan sanda da ke Ilasan don daukar hukunci da bincike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel