NDLEA ta kame wasu 'yan kasuwa 2 dauke da hodar iblis kilogram 3

NDLEA ta kame wasu 'yan kasuwa 2 dauke da hodar iblis kilogram 3

- NDLEA ta kame wasu bata-gari a jihar Legas da babban birnin tarayya Abuja da muggan kwayoyi

- An kame mutanen dauke da hodar iblis kunshe cikin kayayyakinsu da ya kai kiligram 3

- Shugaban rundunar NDLEA ya yabawa jami'an tare da karfafa musu gwiwa kan aikinsu

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wani dan kasuwa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe (NAIA), Abuja da wani mutum a filin jirgin saman Murtala Mohammed (MMIA), Lagos, ‘tare da hodar iblis mai nauyin kilogram uku.’

Mai magana da yawun hukumar, Mista Jonah Achema, ya fada a ranar Alhamis a Abuja cewa yayin da “aka kama Adeleke Kazeem Biola a filin jirgin saman Legas tare da kilogram 1.5 na hodar Iblis a ranar Laraba, 3 ga Fabrairu 2021 a yayin tantance fasinjoji a jirgin Emirate zuwa Dubai.

"Wani dan kasuwa mazaunin Legas, Onu Oluchukwu Juma’a, an kama shi da kilogram 1.527 na miyagun kwayoyi a filin jirgin saman Abuja.” Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Zamu iya gayyatar mayakan kasashen waje su lalata Najeriya, Jagoran 'yan ta'adda

NDLEA ta kame wasu 'yan kasuwa 2 dauke da hodar iblis kilogram 3
NDLEA ta kame wasu 'yan kasuwa 2 dauke da hodar iblis kilogram 3 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya ruwaito kwamandan, MMIA Command na NDLEA, Mista Ahmadu Garba, yana cewa wanda ake zargin, Adeleke "an kama shi ne a farfajiyar tashi daga filin jirgin saman Legas tare da boye kwayar da kyau a cikin kasan jakar tafiya."

Garba ya yarda cewa jerin kame-kamen da aka yi cikin makonni uku da suka gabata ya biyo bayan mummunan matakin da rundunarsa ta dauka ne bisa umarnin sabon Shugaban Hukumar, Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya).

A nasa bangaren, shugaban hukumar, Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba wa kwamandojin filayen jiragen sama na Legas da na Abuja da tawagarsu kan yadda suka yi aikinsu cikin kulawa.

Ya kuma bukace su da su kara himma domin aikin da zai kawar da kasar daga annoba ta haramtattun magunguna.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Legas za ta fatattaki masu talla a kan titunan jihar

A wani labarin, Wasu ‘yan daba da ake zargin 'yan fasa-kwabri ne a ranar Talata sun kai hari tare da raunata wasu jami’ai uku na Hukumar Kula da Ayyukan Tarayya (FOU), Zone A na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NSC) da kuma wani jami’in soja a Legas, The Nation ta ruwaito.

Jami'an, binciken ya nuna cewa, suna kan aikin sintiri ne a kan babban titin Legas zuwa Abeokuta kafin a far musu tare da ji musu rauni.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel