An kama 'yan Najeriya biyar a kasar India ma 'miyagun kwayoyi,da kuma fataucin mutane

An kama 'yan Najeriya biyar a kasar India ma 'miyagun kwayoyi,da kuma fataucin mutane

'Yan sandan India sun kama 'yan Najeriya biyar, bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi.

'Yan Najeriyan - Cosmas Ojukwu, 30; John Okorie, 26; Okereke Cyril Anezi, 31; John Paul Onyebuchi, 34 da kuma Ogunka Henry Okechukwu, 31 - da aka kama bisa zargin kasancewa a cikin mallaki wasu iren-iren kwayoyi, ciki har da hodar Iblis, ruwan kasa sukari da kuma amphetamine.

NAN, ya rawaito cewa Times of India, ta yi rahoton cewa an kuma zargen su da fataucin yan adam ta hanyar miƙa matan Nijeriya ta cikin karuwanci.

'Yan sandan Rachakonda a Hyderabad suka kama su tare da Palaparthi Sangeetha, 35,mataimakin su dan India.

An kama 'yan Nijeriya biyar a kasar India ma 'miyagun kwayoyi,da kuma fataucin mutane'.
An kama 'yan Nijeriya biyar a kasar India ma 'miyagun kwayoyi,da kuma fataucin mutane'.

Anezi wanda shine shugaban 'yan Najeriya a Hyderabad kuma dalibi ne a Nizam College tare da Okorie.

Sangeetha da Onyebuchi sune farko da aka kama - a wata tashar bas a ranar Lahadi "tare da grams uku na hodar Iblis da kuma grams dari biyu na ganja a mallakarsu".

KU KARANTA KUMA: Kotu ta yanke ma wani mutumi hukunci bisa laifin satar kaji

"Bisa ikirarin da Sangeetha da Onyebuchi suka yi, 'yan sanda sun kai ziyara gidansa kuma suka kama shi da hodar Iblis gram goma,sugar ruwan kasa gram goma sha biyu,Allunan amphetamine shude guda talatin da bakwai,da kuma Allunan amphetamine pink,kwamfuta, 1.54 lakh kudin india,wayoyi guda uku da kuma wani abin hawa a mahallinsa, " rahoton yace.

kwamishinan 'yan sandan Rachakonda,Mahesh Bhagawat,ya ce Cosmas ya samun kwayoyi daga abokinsa Gabriel, "wanda yake samu daga Goa da kuma Hyderabad. Yana siyar dasu kwayoyin ta hanyar Sangeetha, John Paul da Henry ".

Ta hanyar ikirarin shi ne 'yan sanda suka ziyarci gidan Okorie, Onyebuchi da Okechukwu, kuma suka same su da "gram bakwai na hodar Iblis,gram dari uku na ganja, Rs 50,000 , kwamfuta da kuma wayar salula a mallakarsu".

Jaridar ta kara da cewa jimlar kwayoyi da kuma yawan kudi ta kãma grams ashirin na hodar Iblis,grams goma sha biyu na sugar ruwan kasa, 39,8 grams allunan amphetamine, 1,675 kg na ganja da Rs 2 lakh kudin india.

Onyebuchi da Okechukwu sun shaida cewa,bugu da kari suna suna fataucin matan Nijeriya wa abokan cinikin su a yakunan Kushaiguda da Neredmet.

Kwamishinan 'yan sanda da aka nakalto sun ce visan tafiyarsu Onyebuchi da Okechukwu India ya kare tun shekarun da suka wuce.

"Yan sandan Mapusa na Goa sun kama John Paul sau biyu a shekara ta 2016 domin ba bisa doka ba ne zama da miyagun ƙwayoyi. Duk da sanin wannan duka, Cyril ya bashi gurun zama a gidan hayar sa," ya ce.

Cosmas, wanda ya zo India a shekarar 2012, a gwargwadon rahoto yana da alaka da masu siyar da miyagun ƙwayoyi da suke nan cikin Goa, Mumbai kuma Chennai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng