Kasurgumin Ɗan Bindiga da Wasu 4 Sun Mutu Yayin Arangama da Junansu a Katsina

Kasurgumin Ɗan Bindiga da Wasu 4 Sun Mutu Yayin Arangama da Junansu a Katsina

  • Kasurguman ƴan bindiga da dama sun rasa rayukansu a jihar Katsina yayin wata mummunan arangama da abokan gaba
  • Daga cikin wadanda suka mutun akwai hatsabibin ɗan bindiga, Usman Modi Modi da sauran ƴan ta'adda guda hudu
  • Sakataren yada labaran gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaulaha shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a yau Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Kasurgumin ɗan bindiga, Usman Modi Modi ya rasa ransa yayin arangama da abokan gaba a jihar Katsina.

Hatsabibin ɗan ta'addan da aka fi sani da Kartakwa ya gamu da ajalinsa ne a jiya Talata 14 ga watan Mayu yayin artabun.

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa na ƙona mutane suna sallah a Kano," Wanda ake zargi ya faɗi gaskiya

Hatsabiban ƴan bindiga sun mutu yayin artabu da juna a Katsina
Yan bindiga da dama sun rasa rayukansu yayin arangama da juna a Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Asali: Facebook

Ƴan bindiga da aka hallaka a Katsina

Yayin harin da ya yi ajalin Modi Modi, an kuma hallaka wasu hatsabiban 'yan bindiga guda hudu, a cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Mohammed ya fitar a yau Laraba 15 ga watan Mayu.

Kaula ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na rana tsakanin Modi Modi na tsagin Kanta da kuma Abdulkarim Faca Faca na tsagin Marina, cewar Vanguard.

Ƴan bindiga da dama sun sami raunuka

"Yayin artabun, Usman Modi Modi da sauran ƴan bindiga hudu sun rasa rayukansu."
"Daga cikinsu akwai Mankare da Gunki Ummadau da Dogo Jabi Birinya na karamar hukumar Kurfi da Harisu Babba Yauni na karamar hukumar Safana."
"Usman Modi Modi da mukarrabansa sun addabi ƙauyukan kananan hukumomin Safana da Kurfi yayin da Abdulkarim Faca Faca ya mamaye kananan hukumomin Batsari da Safana da Marina."

Kara karanta wannan

Bulaliyar kan hanya: Tinubu, Shettima za su fara biyan harajin fakin a filin jirgin sama

"Daga cikin ƴan ta'adda, Usaini Yauni da ke karamar hukumar Safana da Abdulrahman Jankare na Gangare a Tsaskiya sun samu munanan raunuka."

- Ibrahim Kaulaha

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojojin Nigeria ta hallaka 'yan bindiga hudu a wani mummunan farmaki a jihar Kaduna.

Dakarun 'Operation Whirl Punch da ke Arewa maso Yamma sun yi nasarar hallaka miyagu ciki har da kasurgumin ɗan bindiga, Dogo Bangaje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel