Rai banza: Dan damben boksin ya kashe abokin karawarsa da kwakkwaran naushi

Rai banza: Dan damben boksin ya kashe abokin karawarsa da kwakkwaran naushi

Wani shahararren dan damben boksin, Patrick Day ya gamu da ajalinsa a ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba sakamakon rauni daya samu a kwakwalwarsa bayan dukan tsiya daya ci a hannun abokin karawarsa, Charles Conwell.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa Day dan shekara 27 ya shiga halin rai fakwai mutu fakwai na tsawon kwanaki 4 tun bayan dukan da ya ci a hannun Conwell a ranar Asabar din data gabata.

KU KARANTA: An gurfanar da iyaye kan aurar da diyarsu mai ciki ga wani saurayi a Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito karawa tsakanin Day da Conwell ta kai zagaye na 10, inda a nan ne Conwell ya samu sa’ar Day da wata naushin kifa daya kwala, nan take ya zube, daga bisani aka garzaya dashi asibitin Northwestern memorial inda aka yi masa aikin kwakwalwa.

“A ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba ne Patrick Day ya mutu sakamakon rauni daya samu a kwakwalwarsa a damben da ya yi da Charles Conwell a ranar Asabara, 12 ga watan Oktoba a filin dambe na Wintrust dake Chicago Illinois.

“Iyalan Day, da kuma yan uwa da abokan arzikinsa, ciki har da amininsa, kuma maigidansa Joe Higgins suna zagaye dashi a lokacin daya mutu, a madadin iyalan Day, tawagarsa da kuma aminansa, muna godiya da irin addu’o’in da kuka yi masa da kuma kauna da goyon bayan da kuka nuna masa.” Inji mai daukan nauyinsa, Lou DiBella.

Sai dai ba’a kan Day farau ba, inda ko a watan Yulin data gabata, sai da wani karamin dan dambe mai shekaru 23, Hugo Santillan dan kasar Ajantina ya mutu ana tsaka da wasan dambe, yayin da shima Maxim Dadashev dan kasar Rasha ya mutu kwanaki kafin mutuwar Hugo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng