Usyk ya doke ‘Dan damben Najeriya, Anthony Joshua, ya rasa $15m da kambun Duniya

Usyk ya doke ‘Dan damben Najeriya, Anthony Joshua, ya rasa $15m da kambun Duniya

  • Anthony Joshua ya yi magana game da damben da ya yi da Oleksandr Usyk
  • AJ yace nan gaba za su sake hadu wa da ‘dan wasan da ya karbe masa kambu
  • A dambensa da Usyk, Anthony Joshua yace sai da ta kai idanunsa sun rufe

UK - Punch ta rahoto tsohon gwarzon WBA, IBF, da WBO, Anthony Joshua, yana cewa ya koyi darasi a fadan da ya yi da Oleksandr Usyk, inda ya sha kashi.

‘Dan damben kasar Ukraine, Oleksandr Usyk ya doke Anthony Joshua a gwabzawar da suka yi a babban filin wasa na Tottenham Hotspur da ke birnin Landan.

Jaridar tace Usyk ya samu nasara 117-112, 116-112, da 115-113 a kan Joshua a ranar Asabar. Rahotanni sun ce hakan ya sa Joshua ya rasa Dala miliyan 15.

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Attajirin Duniya Elon Musk Da Grimes Sun Rabu Shekara Ɗaya Bayan Haihuwar Ɗansu Mai Suna X Æ A-Xii

Da yake bayanin yadda ya sha kashi a hannun abokin damben na sa, Anthony Joshua yace da aka je zagaye na tara, sai ta kai idanuwansa ba su iya ganin komai.

An rahoto AJ yana cewa zai yi tanadi da kyau, ya kara samun horo domin ya sake hadu wa da abokin fadan na sa, yace idanunsa ba su taba rufe wa a dambe ba.

Anthony Joshua
Anthony Joshua Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Akwai wani jikon

“Ina taya wanda ya yi nasara murna. Za mu sake hadu wa. A koma bakin aiki. Zagaye 12 sun yi kyau, na dauki darasi a filin dambe.”
“Za mu cigaba daga inda aka tsaya, nan ba da dade wa ba za mu sake gwabza wa.”
“Ta kai ban iya gani a zagaye na tara, na daina ganin komai. Amma dai na dauki darasi ko a cikin runtsi, dole ne ka rike kanka.”

Kara karanta wannan

Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure

“Wannan ne karon farko da idanuna suka rufe a wurin fada. Da ido daya na koma kallo. Amma daga baya abubuwa sun farfado.”

AJ yace zai yi kokari ya gyara kura-kuransa idan sun sake hadu wa, a cewarsa ba ta abokin fadarsa yake ba, ya fi damu wa da toshe kafar da ya bari a dambensa.

Ronaldo yana karbar albashi mai tsoka

Kwanakin baya ku ka ji Cristiano Ronaldo ya zama ‘dan wasan kwallon kafan da ya fi kowa karbar albashi mai yawa a kasar Ingila, bayan komawarsa Ingila.

Kungiyar Man United za ta rika biyan Cristiano Ronaldo kusan Naira miliyan 38 a kullum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel