Kaico: Dauda Ya Kashe Dan Uwansa Yayin Dambe Kan N1,000 A Legas

Kaico: Dauda Ya Kashe Dan Uwansa Yayin Dambe Kan N1,000 A Legas

  • Wani mai suna Ibrahim ya hallaka dan uwansa har lahira akan N1,000 a Legas biyo bayan cacar baki
  • Al'umma sun yi kokarin ceto rayuwar mamacin ta hanyar kai shi asibitin sai dai zuwan su asibiti likita ya shaida musu mutuwar sa
  • Har zuwa lokacin kammala wannan rahoton ba a samu damar jin ta bakin rundunar yan sandan Jihar Legas akan lamarin ba

Legas - Wani mutum, Ibrahim Dauda, ana zargin ya kashe dan uwansa, Tunde, lokacin da suke fada akan N1,000 a gidansu da ke layin Amusa, kusa da babban titi, na yankin Obadore da ke Igando, Jihar Lagos.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ibrahim da Tunde suna gida lokacin da cacar baki ta barke tsakaninsu akan N1,000.

Rundunar yan sanda
Kaico: Dauda Ya Kashe Dan Uwansa Yayin Dambe Kan N1,000 A Legas. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun koma kwana gindin ATM saboda tsananin rashin kudi

Yadda lamarin ya faru

Wakilin Punch ya shaida cewa cacar bakin ta yi kamari har suka fara fada inda Ibrahim ya yi gudu ya dauko wani karfe a gidan.

Yana zuwa, Ibrahim yayi amfani da karfen rodin ya makawa Tunde a goshi inda anan take mai shekaru 27 ya fita daga hayyacinsa ya kuma fadi.

Wata majiya, ta shaidawa wakilinmu, yayin da ake kokarin ceto rayuwar Tunde, mutane sun garzaya da shi babban asibitin Igando, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Majiyar ta ce:

''Lamarin ya faru ranar Lahadi, 29 ga Janairu, 2023. Su na fada ne akan N1,000 kuma ana haka ne, daya a cikin su (Ibrahim) ya yi amfani da rodi ya bugawa dan uwansa (Tunde) a goshi.
''Mutane sun yi gaggawar kai shi asibiti a Igando amma da suka je an tabbatar musu ya mutu. Sai suka mayar da gawarsa babban asibin Mainland, da ke Yaba, don binciken gawa.''

Kara karanta wannan

Yadda Dan Shekara 20 Mai Koyon Sana'a Ya Kashe Mai Gidansa, Ya Jefa Gawarsa Cikin Rijiya

Yan sanda sun kama Ibrahim

Wakilin majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa yan sandan Igando sun kama Ibrahim.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda, SP Benjamin Hundeyin, bai daga waya ba kuma bai dawo da martanin gajeran sakon da aka aika masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton ranar Litinin.

Magidanci ya halaka matarsa da duka saboda burodi a Legas

A wani rahoton kun ji cewa wani Ndubisi Uwadiegwu ya halaka matarsa mai suna Ogochukwu Enene da duka saboda burodi.

Rahotanni sun nuna cewa ta bukaci ya siya musu burodi a gida amma ya nuna ba shi da kudi sai ta yi amfani da kudinta ta siya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel