Al Mustapha ya Baro Aiki, Ya Ce Duk Wanda ya Taba Fetur Zai Yi Wuya ya Dade a Mulki

Al Mustapha ya Baro Aiki, Ya Ce Duk Wanda ya Taba Fetur Zai Yi Wuya ya Dade a Mulki

  • Hamza Al-Mustapha ya yi kira ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jajirce wajen magance matsalolin da suka addabi Najeriya
  • Tsohon sojan ya nuna ba za a rasa alaka tsakanin arzikin Najeriya da kasuwancin mai da kamfanoni da kasashe duniya ba
  • Manjo Al-Mustapha mai ritaya ya ce bai kamata kasa irin Najeriya ta rasa wutar lantarki ba saboda dibin arzikin da take da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hamza Al-Mustapha ya yi wata magana da ta za ta iya zama hannunka mai sanda ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu mai-ci.

Dogarin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya nuna sai an yi hattara da ‘yan kasuwa.

Al-Mustapha
Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce ana iya yi wa shugaban kasa zagon kasa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Hamza Al-Mustapha ya bayyana hadarin mala'u

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya a wata hira da ya yi da tashar DCL Hausa ya ce masu harkar fetur za su iya rusa gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon sojan ya ce ‘yan kasuwan mai za suyi duk abin da za su iya domin kare dukiyar aljihunsu duk da karfin shugabannin kasar.

‘Dan takaran shugaban kasar ya ce dole sai an bi lamarin mai da hikima da tunani, a kawo masana, domin za a iya shirya zagon-kasa.

Al-Mustapha yana so Tinubu ya guji IMF

Sojan ya ce a kauracewa irinsu IMF da bankin duniya da sharudan da suka kakabawa Najeriya a 1986 a zamanin Ibrahim Babangida.

A kalamansa, ya tabo zancen wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta kara kudinsa kwanan nan, ya kawo yadda za a magance matsalar.

Hamza Al-Mustapha yana ganin babu dalilin da za a rasa wuta a Najeriya, ko a ce sai al’umma sun kashe makudan kudi kafin su ga haske.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya yi rashin nasara a babbar kotun tarayya

Da gaske Najeriya ce ta 2 a gas a duniya?

A duk duniya, Najeriya ce ta biyu a arzikin gas wanda ake amfani da shi wajen samun wutar lantarki a cewar tsohon Manjon sojan.

Al-Mustapha ya ce Najeriya tana da ruwa, hasken rana, iska da ma’adanai wadanda duk za su iya amfani wajen samun wutar lantarki.

Legit ta binciki ikirarin, ta gano cewa duk da Najeriya tana da albarkar gas, kuma kasar Rasha ce a gaba, amma ba ita ce ta biyu ba.

Bayanan shafin Worldmeter ya nuna Iran ce ta biyu a arzikin gas, Najeriya ce ta tara.

Najeriya tana bayan Amurka, Qatar, Saudi da tarayyar Larabawa. Arzikin gas da ake da shi bai kai yadda Al-Mustapha yake fada ba.

Yadda aka nemi Tinubu aka rasa

Kwanaki aka ji labarin an shafe mako guda kenan da tashi taron tattalin arziki da aka yi a birnin Riyadh, ba a ga Bola Tinubu ba.

Daga Nederland, Bola Ahmed Tinubu ya wuce zuwa Saudiyya kuma ya dade bai dawo Abuja ba, hakan ya jawo wasu suka shiga dar-dar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel