Dan Ta’addan Boko Haram Ya Mika Wuya a Borno, Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 135
- A yayin da rundunar sojin Najeriya ke kara kaimi wajen yaki da ta'addanci, wani dan ta'addan Boko Haram ya mika wuya a jihar Borno
- Dan ta'addan mai suna Alhaji Wosai ya mika wuya ne a ranar 11 ga watan Mayu inda ya mika bindiga kirar Ak47 guda daya da alburusai
- A hannu daya kuma, sojojin sama da na kasa sun kashe 'yan bindiga 135, sun kama 182, tare da ceto mutane 140 da aka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Borno - Wani dan ta'addar Boko Haram mai suna Alhaji Wosai ya mika wuya ga sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai.
Dan ta'addan Boko Haram ya mika wuya
An ce dan ta’addan ya mika wuya ne a ranar 11 ga Mayun 2024, ga dakarun soji na 21 (Armored Brigade) bayan ya tsere daga maboyar ‘yan ta’addan a kauyen Garno da ke jihar Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar leken asiri ta sanar da Zagazola Makama cewa ya mika wuya da bindiga kirar AK 47 da kuma gidan harsashi guda daya wanda ke cike da harsashi kirar 7.63mm.
A halin yanzu dai dan ta'addan yana hannun sojoji inda ake nadar bayanansa da kuma neman sahihan bayanai kan tsofaffin abokansa da ke aikata laifi a yankin.
Sojoji sun kashe 'yan bindiga 135
Hedikwatar tsaro ta ce sojojin sama da na kasa sun kashe 'yan bindiga 135, sun kama 182, tare da ceto mutane 140 da aka yi garkuwa da su a fadin kasar a makon jiya.
Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja kan ayyukan rundunar sojin kasar.
Buba ya ce sojojin sun kwato makamai iri-iri har guda 97 da alburusai iri-iri har guda 3,117 a cikin makon.
Sojoji sun kwato makamai da kudi
Ya ce kayayyakin da aka kwato sun hada da bindigogi kirar AK47 guda 47, PKMG daya, bindiga FN daya, bindigu na gida guda 17, jaridar Vangaurd ta ruwaito.
Sauran sun hada da bindigogin Dane guda 21, bindigogin fanfo guda 9, bindigogi kirar baushe guda uku, gurneti 3×36, da kuma IED guda daya.
Baya ga makamai da alburusai, rundunar ta kwato motoci 15, babura 21, kekuna shida, wayoyin hannu 43, da kuma kudi Naira miliyan 2.02, da dai sauransu.
'Yan bindiga sun sace dalibai a Kogi
A wani labarin, mun ruwaito maku cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kai hari jami'ar kimiyya da fasaha ta Confluence (CUSTEC) da ke jihar Kogi.
A yayin harin, sun yi awon gaba da dalibai da dama bayan da suka kutsa har cikin ajujuwan karatun daliban tare da bude wuta kan mai uwa da wabi.
Asali: Legit.ng