Tinubu: Bayan Watanni da Magana, Kashim Shettima Ya Maidawa Atiku Martani

Tinubu: Bayan Watanni da Magana, Kashim Shettima Ya Maidawa Atiku Martani

  • Kashim Shettima bai ganin Argentina wata abin koyi ce da za a ba shugabannin Najeriya shawarar su bi sahun gwamnatin kasar
  • Mataimakin shugaban kasar Najeriyan ya halarci wani taro da aka shirya a Abuja, ya yi bayanin nasarorin Bola Tinubu a ofis
  • Sanata Kashim Shettima ya yi raddi a kaikaice ga Alhaji Atiku Abubakar wanda ya taba kawo shawarar ayi koyi da Javier Milei

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kashim Shettima ya yi wata magana da za ta iya zama martani ga jagoran adawa a Najeriya watau Alhaji Atiku Abubakar.

Mataimakin shugaban Najeriyan ya yi wannan raddi ne ga Atiku Abubakar a dalilin kira da ya yi ga gwamnati tayi koyi da Argentina.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Kashim Shettima da Atiku Abubakar
Kashim Shettima ya soki Atiku Abubakar wajen kare Bola Tinubu a Abuja Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A wajen wani taro na musamman da 21st Century Chronicle ta shirya, Sanata Kashim Shettima ya yarda ya zama babban mai jawabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima ya caccaki Atiku Abubakar?

Mataimakin shugaban kasar bai kama suna ba, amma ya soki wanda ya yi kira ga gwamnati ta dauki darasi daga shugaban Argentina.

A baya an ji Atiku Abubakar yana cewa kyau sabon shugaban Argentina ya zama abin koyi ga Bola Tinubu a farfado da tattalin arziki.

Shettima ya ce abubuwa sun sukurkucewa Argentina

Kamar yadda Mahmud Jega ya kawo labarin a rubutun da ya yi a jaridar, ya ce Shettima ya ce kasar nahiyar Amurkan ba abin koyi ba ce.

A cikin makonni biyu, ana kallo farashin kayayyaki suka tashi a Argentina, Shettima ya ce an gagara fahimtar kasashen sun sha bam-bam.

Kara karanta wannan

"Sun lalata komai": Tsohon shugaban kasa ya koka yadda aka ruguza ayyukansa

Najeriya tana cikin mawuyacin hali, amma tsohon gwamnan na Borno ya yi wa al’umma alkawari za a shawo kan tattalin arzikin kasar.

Ba a tashi taron ba sai da Shettima ya yabi Nuhu Ribadu da Yemi Cardoso saboda kokarinsu wajen yakar masu hana Naira daraja.

Cigaban da gwamnatin Tinubu ta samu

Daga cikin nasarorin da ya ce gwamnatin Tinubu ta samu akwai kawocigaban tattalin arziki, samar da abinci da kuma yaki da talauci.

Sannan ya ce ana kamanta bin dokar kasa, yaki da rashin gaskiya tare da tafita da kowa.

Atiku ya kawo misali da Javier Milei

A baya an rahoto yadda sabon shugaban Argentina ya karbi mulki kamar yadda Bola Tinubu ya gaji Muhammadu Buhari a Mayun 2023.

Javier Milei ya ci karo da matsalar tsadar kaya, yawan bashi da talauci, amma ya kama hanyar gyara kasarsa a cewar Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel