Takaittun Abubuwa 10 da Ya Kamata Ku Sani Game da Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP, Alhaji Atiku Abubakar

Takaittun Abubuwa 10 da Ya Kamata Ku Sani Game da Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP, Alhaji Atiku Abubakar

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP na daya daga cikin wadanda idan za a rubuta tarihin Najeriya, dole a ambaci sunayensu.

To amma, meye kuka sani game da dan takarar da ke son gaje shugaba Muhammadu Buhari a zaben ranar Asabar 25 ga watan Faburairun 2023?

Legit.ng Hausa ta yi duba tare da yin waiwaye ga rayuwar Atiku kacokan tare da kawo muku takaitaccen rahoto.

Gwabzawar zaben bana

Kasa da sa’o’i 24 ne suka rage a yi zaben shugaban kasa a Najeriya don zabo wanda zai ci gaba da rike ragamar kasar.

Dukkan ‘yan takara 18 sun shirya tsaf, ‘yan Najeriya miliyan 87.2 sun shirya su ma rike da katin zabe na PVC.

Tarihin dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar
Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a PDP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa: Karfi da Raunin Tinubu, Atiku, Obi, Kwankwaso a Zaben Ranar Asabar

A bangare guda, ‘yan takara hudu ne na shugaban kasa suka fi sanuwa tare da zama fitattu a kasar, kuma kowa daga cikinsu na hango nasara a zaben na bana.

Wadannan ‘yan takarar sun hada Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na Labour da kuma Rabiu Kwankwaso na NNPP.

A wannan makalar, Legit.ng Hausa ta mai da hankali ne ga rayuwar dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar. Ga kadan daga abubuwan da ya kamata ku sani game dashi:

1. Shekaru da rayuwar Atiku

Shekarunsa 76, an haifi Atiku Abubakar a ranar 25 ga watan Nuwamban 1946 a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas, dan siyasa ne kuma hamshakin dan kasuwa, rahoton BBC.

2. Karatunsa

Duk da cewa mahaifinsa na da kiyayya ga ilimin boko, Atiku ya yi firamare da sakandare a jihar Adamawa.

Ya yi difiloma a jami’ar Ahmadu Bello inda ya karanta ilimin shari’a kafin daga bisani ya yi digiri na biyu a jami’ar Anglia Ruskin, Cambridge da ke Burtaniya.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso Za Su Raba Kuri’u Miliyan 87 Nan da Awa 24

3. Rasuwar mahaifinsa

Yana da shekaru 11 a duniya, Atiku ya rasa mahaifinsa Malam Garba Atiku Abdulkadir, kuma ya kasance da tilo ga iyayen nasa.

4. Aurensa da ‘ya’yansa

Bayanai sun nuna cewa, Atiku ya yi aure har sau biyar amma ya taba yin saki sau daya. A halin da ake ciki, yana da mata hudu da ‘ya’ya 28.

5. Rayuwarsa kafin shiga siyasa

Kafin ya zama dan siyasa a Najeriya, Atiku ya kasance fitaccen jami’in hukumar kwastam, inda ya taka rawar gani a jihar Legas har ya kai shakaru 43 a duniya, ya shiga siyasa.

6. Takarar gwamna

Atiku ya yi takarar gwamnan jihar Adamawa a shekarar 1990, 1996 da kuma 1998, inda ya yi nasara daga karshe.

7. Ya zama mataimakin shugaban kasa

Daga bisani, an dauki Atiku ya zama mataimakin shugaban kasa ga Olusegun Obansajo a shekarar 1999, suka yi tazarce a shekarar 2003.

Kara karanta wannan

Jerin Jihohi 6 da Za a Fafata da Gaske Tsakanin ‘Yan Takaran Shugaban Kasa

8. Ya yi takarar shugaban kasa sau da yawa

Atiku ya yi takarar shugaban kasa a Najeriya har sau biyar; 1993, 2007, 2011, 2015 da kuma 2019.

Ya yi takararsa ne a karkashin jam’iyyar AC a 2007, PDP a shekarar 2011, a 2014 ya shiga APC ta su Buhari, nan ma aka ba Buhari tikitin zaben 2015, sai kuma a 2019, ya sake fitowa a PDP.

9. Zaben 2023 da takararsa

A wannan karon, 2023, Atiku ya sake fitowa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP mai adawa, a karo na shida kenan.

10. Lambobin yabo da kwazonsa

Atiku Abubakar ya samu lambobin yabo daga kungiyoyi daban-daban na duniya, musamman a fannin wanzar da zaman lafiya, ciki har da National Peace Corps Association (NPCA).

Asali: Legit.ng

Online view pixel