Kamfani Ya Maka Ma’aikata 2 Gaban Kotu Bisa Zargin Satar Biredin N2,600
- Wani babban kanti a jihar Oyo ya gurfanar da wasu ma’aikatansa biyu a gaban kotu bisa zargin satar biredi biyu da kudinsu ya kai N2,600
- Kamfanin ya garzaya kotu kan cewa ma’aikatan, wadanda suka ki amsa laifinsu, sun hada baki tare da yi masa sata a lokacin da ba kowa
- Kotun majistare ta bukaci wadanda ake tuhumar da su biya tarar Naira 50,000 yayin da aka dage sauraron karar zuwa wani lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Oyo - An gurfanar da wasu ma’aikatan kamfanin FoodCo guda biyu da ke Ringroad a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a gaban kotun majistare ta Iyaganku.
Kamfanin FoodCo ya gurfanar da ma’aikatan ne kan zargin sun hada baki tare da satar masa biredi guda biyu a kantin kamfanin.
'Satar biredi': Kamfani ya gurfanar da ma'aikata
Wadanda ake zargin, Ebenezer Olusesi mai shekaru 31 da kuma Ibrahim Adeniyi mai shekaru 41, sun ki amsa laifin satar biredin da kudinsu ya kai N2,600, jaridar The Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan mai gabatar da kara, Cpl. David Adepoju, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki ne tare da satar kayan a ranar 28 ga Afrilu.
Adepoju ya kara da cewa laifin ya sabawa dokar laifuffuka ta jihar ta 2000 a karkashin sashe na 390 (a) da na 516.
Belin ma'aikatan da ake zargi da satar biredi
Jaridar PM News ta ruwaito alkaliyar kotun, Misis Olabisi Ogunkanmi, ta amince da bukatar bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan kudi N50,000 kowannen su tare da tsayayyu biyu.
Kotun ta kara da cewa dole ne daya daga cikin wadanda za su tsaya masa ya gabatar da shaidar haraji na akalla shekaru biyu, yayin da daya kuma ya kasance dan uwa.
Daga nan aka dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Agusta domin sauraren shari'ar.
Rigimar Fatima Mai Zogala da Aisha
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wakar da Dauka Kahutu Rarara ya yi wa wata Fatima Mai Zogala ta bar baya da kura tsakanin Fatima da uwar dakinta Aisha.
Bayan wakar Rarara ta fasa gari, an ruwaito Aisha ta kori Fatima daga shagonta, daga baya kuma ta musanta wannan zargi, sai dai ita Fatima ta gasgata hakan ga manema labarai.
Fatima ta bayyana cewa tun bayan da wani abokin cinikinta ya ba ta kyautar turamen zani domin ta dinka da mahaifiyarta, Aisha ta nemi ta ba ta daya ta hana, suka samu sabani.
Asali: Legit.ng