Yadda Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Duka Saboda Biredi A Legas

Yadda Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Duka Saboda Biredi A Legas

  • Wani lamari mara dadi ya faru a Legas a yayin da wani magidanci Ndubisi Uwadiegwu ya halaka matarsa Ogochukwu saboda biredi
  • Wata sanarwa ta ce babban dan marigayiyan dan shekara 14 ya ce mahaifinsu ya yi amfani da madubi ya yi wa mahaifiyarsu duka har ta mutu
  • Rahotanni ya nuna cewa ta bukaci ya siya musu biredi da yara amma ya ce bai da kudi, ta cire kudinta ta siya biredi daya kuma ya shiga kicen ya cinye baki daya, da ta yi magana ya kama ta da duka

Jihar Legas - Wani mutum mai suna Ndubisi Uwadiegwu, dan asalin jihar Enugu ya yi wa matarsa, Ogochukwu Enene, duka har ta mutu saboda biredi, rahoton The Punch.

An tattaro cewa marigayiyan yar asalin kauyen Umuokpu, Awka ne a jihar Anambra, amma ta auri mijinta dan jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Wani matashi ya yi tsaurin ido, ya sace mahaifinsa, an ba kudin fansa N2.5m

Burodi
Yadda Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Duka Saboda Biredi A Legas. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

A cewar wani rahoto a intanet da Punch ta samu a ranar Lahadi, dan marigayiyar dan shekara 14, ya ce mahaifinsu ya doki mahaifiyarsu da madubi har ta mutu, saboda ta fada masa ya siya musu biredi amma ya ce ba shi da kudi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan ya kara da cewa mahaifiyarsa ta siya biredi daya da kudinta don yaran, amma mahaifin ya shiga kicin ya cinye biredin baki daya, kuma da mahaifiyarsu ta tambaye shi dalilin da ya cinye biredin, sai ya fara dukanta hakan ya yi sanadin mutuwarta.

Duk da cewa kawo yanzu iyalan ba su yi tsokaci a hukumance kan lamarin ba, wata majiya kusa da yan uwan ya tabbatarwa majiyar Legit.ng Hausa cewa lamarin ya faru a Legas.

Majiyar, mace, ta ce marigayiyar "Senior Prefect" ne a makarantar sakandare ta mata na Amenyi Girls a shekarar 2000.

Kara karanta wannan

Wani Magidanci, Nuhu Usman, Ya Bindige Matarsa Har Lahira A Bauchi

Yadda abin ya faru

Ta ce:

"Don Allah kungiyar tsaffin daliban makarantar GSSA, Ogochukwu na bukatar adalci."

Sanarwar da aka wallafa a intanet ta ce:

"Wannan ita ce ADA Awka mai suna Ogochukwu Anene daga kauyen Umuokpu a kauyen Awka."

Ta auri wani Mr Ndubisi Uwadiegwu daga Jihar Enugu wanda ya kashe ta duka kuma yana shirin birne ta ba tare da sanar da yan uwanta yadda ya dace ba.

Sanarwar ya cigaba da cewa:

"Ogo tana da yaya biyar, hudu maza da mace daya. Danta na farko shekararsa 14 ya ce mahaifinsu ya yi amfani da madubi ya yi wa mahaifiyarsu duka saboda ta ce ya siya musu biredi kuma ya ce ba shi da kudi.
"Da mahaifiyarsu ta yi amfani da kudinta ta siya biredi daya, mahaifin ya tafi kicin ya cinye biredin baki daya kuma da ta yi tambayan dalilin da yasa ya cinye biredin baki daya ba tare da rage wayara ba, ya fara dukanta, hakan ya yi sanadin mutuwarta.

Kara karanta wannan

Shekarun Diyata 4 Kacal: Magidanci Dan Shekaru 50 Ya Koka Kan Rashin Aure Da Wuri

"Ogochukwu Anene babban 'Prefect' ce a makarantar sakandare ta mata ta Amenyi a 2000."

Asali: Legit.ng

Online view pixel