An yiwa wani mutumi bulala 12 akan ya saci biredi

An yiwa wani mutumi bulala 12 akan ya saci biredi

- Alkalin babbar kotun da ke yankin Zuba a Abuja, Gambo Garba ya yankewa wani mutum hukuncin bulali 12

- Alkalin ya yanke wannan hukuncin ne bayan da aka kama Yakubu Nasiru da laifin balle wani shago tare da yin sata

- Yakubu ya bayyana cewa, tsananin yunwa ce ta sa shi balle shagon tare da satar kwai, biredi, madara da kuma kudi

Alkalin wata babbar kotu dake yankin Zuba a Abuja, Gambo Garba, a ranar Laraba ya yankewa wani karamin barawo hukuncin bulala 12. Alkalin ya yankewa Yakubu Nasiru hukuncin bulalin ne saboda satar da yayi.

Gistmania ta ruwaito cewa, lauyan mai gurfanarwa, Chinedu Ogada, ya sanar da kotun cewa Yakubu Nasiru ya shiga hannu ne bayan koken da wani Aminu Lawal ya kai a ranar 14 ga watan Disamba 2019.

Aminu Lawal ya kai rahoton yadda barawon ya balle shagonshi kuma ya sace kwai, bota, biredi, ledar madara da kuma N1,850 daga asusun shagon.

Mai gurfanarwar ya ce, wanda aka yankewa hukuncin ya amsa laifinshi yayin da jami’an tsaro ke bincike. Ya kara da cewa an samu wasu miyagun makamai daga wajenshi.

KU KARANTA: Da idona na kama mijina akan mai aikin mu yana lalata da ita - Matar aure

A yayin gurfanarwar, wanda aka yankewa hukuncin ya sanar da kotun cewa, yunwa ce ta sa shi balle shagon kuma ya sace kayan. Ya kara da cewa, ya zauna a shagon inda ya soya kwan don ya ci.

Alkali Garba ya bada umarnin a zane Yakubu Nasiru bulali 12 saboda laifin sata.

Ya kara da jan kunnen wanda aka yankewa hukuncin da ya guji aikata irin wadannan laifukan, kuma ya nemi hanyar halas ta samun abin saka wa a bakinshi na salati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel