“Sako Ga Masarautar Zamfara”: ’Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Hadimin Sarki da Suka Sace
- Daya daga cikin wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai makon jiya, ya rokiSarkin Zamfara ya kai masu dauki
- A wani bidiyo da 'yan bindigar suka saki, an ga Alhaji Buhari, wanda ya ce shi ne Shamakin Sarki yana magiya da a taimaka masu
- Shamakin Sarki ya ce sama da mutane 600 ne ke a hannun 'yan bindigar wadanda ke da matukar bukatar agaji domin komawa gida
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Zamfara - Wani bawan Sarkin Zamfara mai suna Alhaji Buhari (Shamaki) a wani faifan bidiyo, ya roki sarkin da ya sa baki domin a sako su.
A makon jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari fadar Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Muhammad Bunu, inda suka kashe mutane uku tare da yin awon gaba da wasu mazauna garin.
'Yan bindiga sun kai hari Zamfara
‘Yan ta’addan, a cewar mazauna yankin, sun kai hari gidan tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Nasarawa, Kanar Bala Muhammad Mande (mai ritaya).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai jami’an tsaro sun yi awon gaba da sarkin zuwa Gusau, kamar yadda jaridar Daily Trust. ta ruwaito.
A cikin faifan bidiyon, an ga mutanen da aka sace an rufe idanuwansu da kyallaye yayin da ‘yan bindiga suka kewaye su.
'Yan bindiga sun saki bidiyo
Bidiyon da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya nuna Shamaki yana rokon Sarkin Zamfara da ya tausaya tare da bayar da taimako wajen sako su.
Alhaji Buhari (Shamaki) ya ce sama da mutane 600 ne ke a hannun 'yan bindigar wadanda ke da matukar bukatar agaji domin su koma su ci gaba da kula da iyalansu.
Shamaki ya nemi taimakon Sarkin Zamfara
Shamaki ya ce:
“Ko ba ka da komai idan ka fita kana dan kwadago za ka samu abin da zaka ciyar da iyalinka. Don girman Allah mai martaba ka ceci talakawannan naka.
"Don Allah Sarkin Zamfara ka dube mu da idon rahama ka ceci talakawanka. Mun haura mutum 600 a cikin dajin nan. Nine shamakinka, Alhaji Buhari."
Kalli bidiyon a kasa:
'Yan bindiga sun kai hari Abuja
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito 'yan bindiga sun kai hari yankin Dutse da ke a karamar hukumar Bwari, babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da mutane hudu.
Wannan harin na zuwa ne makonni da 'yan bindigar suka kai hari yankin tare da sace mutane biyar, lamarin da ke kara nuna tabarbarewar tsaro a yankin.
Asali: Legit.ng