Nasrun MinalLah: Dakarun Sojoji Sun Daƙile Hari, Sun Sheƙe Ƴan Bindiga a Ƙauyen Taraba
- Sojoji da ke atisayen 'Whirl stroke' a jihar Taraba sun samu nasarar dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai kauyen Kweserti da ke Ussa
- A yayin dakile harin ne sojojin suka yi nasarar kashe 'yan bindiga biyu tare da kwato makamai da harsasai yayin da 'yan ta'addan suka tsere
- Haka zalika sojojin bataliya ta 114 da ke karkashin 3C sun kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a yankin Lau da ke jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Tararaba - Dakarun runduna ta 6 da ake kira 'Whirl stroke' sun kashe 'yan ta'adda biyu a yayin da suka dakile wani hari a kauyen Kweserti da ke karamar hukumar Ussa a jihar Taraba.
Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga
Oni Olubodunde, mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 6, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ne ya tabbatar da faruwar lamarin, jaridar The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Olubodunde ya ce:
“Dakarun runduna ta 6, rukuni na 3 da ke atisayen 'Whirl Stroke' sun sake nuna kwazonsu na kawar da ta’addanci da kakkabe masu tayar da kayar baya a jihar Taraba.
“A samamen baya-bayan nan da sojojin suka kai, an samu gagarumar nasara wajen dakile hare-hare, da kama wadanda ake zargi laifin tare da kuma kwato makamai da alburusai."
Sojoji sun kashe 'yan bindiga biyu
Ya kara da cewa:
“Dakarun bataliya ta 93 a karkashin 3B OPWS, sun kaddamar da wasu hare-hare a mabuyar 'yan bindiga a kauyukan Rikwenmakpawere da Alaha dake karamar hukumar Ussa.
"Sojojin sun yi nasarar dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai na mamaye kauyen Kweserti. Bayan musayar wuta, 'yan bindigar sun ranta a na kare."
Ya ce sojojin sun kashe 'yan bindiga guda biyu tare da kwato gidan harsashin bindigar AK-47 guda daya da harsashi na musamman mai tsayin 7.62mm har guda bakwai.
Sojoji sun kama 'yan ta'adda biyu
Channels TV ta rahoto Olubodunde ya ce dakarun bataliya ta 114 da ke karkashin 3C sun kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a karamar hukumar Lau ta jihar.
Ya kara da cewa sojojin sun kwato bindigar SMG guda daya, bindiga kirar 'barrel' guda daya, gidajen harshashin bindigar AK-47 guda biyu, da harsasai na musamman guda 51.
Rundunar sojin ta roki jama’a da su ci gaba da tallafawa sojoji ta hanyar samar da sahihan bayanai a kan lokaci don yakar 'yan bindiga, da duk wani nau’in ta’addanci a jihar.
Filato: Yan bindiga sun mika wuya
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu 'yan bindiga da ba a bayyana adadinsu ba sun mika wuya tare da ajiye makamansu ga gwamnatin jihar Filato.
Gwamnatin jihar ta ce wannan nasara ta biyo bayan doguwar tattaunawar sulhu da 'yan bindigar domin kawo zaman lafiya a garuruwan jihar.
Asali: Legit.ng