Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Mahaifar Ministan Tinubu, Sun Tafka Babbar Barna
- Yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Maradun da ke jihar Zamfara, sun kashe mutane biyu tare da yin awon gaba da wasu 30
- Maradun dai nan ce mahaifar karamin ministan tsaro, Bello Matawalle kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara wanda ya bar gado a 2023
- Ba wannan ne karon farko da 'yan bindiga suka kai hari kauyen ba, mazauna garin sun koka kan ta'azzarar matsalar tsaro a yankunan Maradun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Maradun, jihar Zamfara - Yan bindiga sun kai hari kauyen Maradun, mahaifar karamin ministan tsaro, Bello Matawalle a safiyar ranar Juma'a, 26 ga watan Afrilu.
A yayin harin kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, sun kashe mutane biyu tare da yin awon gaba da akalla mutane 30.
Maradun hedikwata ce ta karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara wacce ke fama da matsalolin tsaro a 'yan kwanakin nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun tafka barna
Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun kai hari kauyen da misalin karfe 2:00 na dare inda suka kwashe awanni biyu suna cin karensu ba babbaka.
Daga cikin wadanda aka yai garkuwa da su akwai mata, kananan yara da dattawa wadanda aka bi su har gida aka yi awon gaba da su, shafin Daily Post ya ruwaito.
Wani mai rike da sarautar gargajiya a kauyen wanda kuma 'yan bindigar suka kutsa gidansa, ya koka kan ta'azzarar tsaro a yankin.
"Muna kwance a cikin gida 'yan bindiga suka shigo suna binciken dakuna da falo. Na yi nasarar boyewa yayin da matana da yara suka bi wata hanyar suka tsere."
- Masarauta
Ta'azzarar matsalar tsaro a Maradun
Jaridar The Punch ta rahoto mai sarautar na cewa a makon da ya gabata ma 'yan bindiga sun kai makamancin wannan farmakin a kauyen.
Shi ma wani mazaunin garin, Hassan Ibrahim ya ce 'yan bindiga sun yi daba daba tare da mamaye garin dauke da muggan makamai.
Ya yi kira ga karamin ministan tsaro, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Zamfara da ya bar gado, da ya kai masu ɗauki kafin 'yan bindigar su karar da su.
Yan bindiga sun halaka shugaban APC
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun kashe Sa'idu Basa, shugaban jam'iyyar APC a gundumar Mai Dabino, jihar Katsina.
An tattaro cewa 'yan bindigar sun farmaki Sa'idu Basa tare da kashe shi a kan hanyarsa ta komawa Mai Dabino bayan dawowa daga wani taron jam'iyyar a garin Dan Musa.
Asali: Legit.ng