Neja: 'Yan Ƙauye Sun Shiga Ɗimuwa Bayan Sojoji Sun Fece Tare Da Barinsu a Hannun 'Yan Bindiga
- Wasu mutanen yankin Allawa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja sun shiga fargaba kan ficewar sojoji a yankin
- An wayi garin yau Alhamis 25 ga watan Afrilu da ganin sojojin da ke yankin suna tattare kayansu domin barin yankin
- Mazauna kauyen sun bayyana fargaba kan matakin inda suka fara guduwa wasu wurare domin neman tsira daga harin 'yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uk.
Jihar Niger - An shiga fargaba bayan sojoji sun tashi daga sansaninsu da ke kauyen Allawa a karamar Hukumar Shiroro a jihar Neja.
Allawa na daga cikin ƙauyukan da ke fama da hare-haren 'yan bindiga wanda ya yi sanadin mutane da dama a yankin.
Yaushe sojoji suka bar kauyen Neja?
Dakarun sojojin sun tattare dukkan kayayyakinsu da ke sansanin tare da barin yankin da ke cikin matsalar tsaro, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ne ya tilasta mazauna yankin da suka hada da dattawa da mata da yara tsallake gidajensu inda suka yi tafiyar kilomita 50 domin neman tsira.
Mazauna yankin sun bayyanawa Daily Trust cewa abin ya zo musu a bazata ganin yadda suke cikin halin kunci na hare-hare.
Suka ce sun wayi garin yau Alhamis 25 ga watan Afrilu inda suka ga sojojin na tattare kayansu da nufin barin yankin da ke fama da harin 'yan bindiga.
Martanin wani mazaunin kauyen a Neja
Wani Malam Yahuza Allawa a yankin ya ce tun karfe 4:00 na asuba suka fara watsewa daga garin zuwa wasu wurare daban.
Yahuza ya ce mafi yawan garuruwan da suke zuwa sun hada da Erena, Gwada, Kuta or Zumba domin samun tsaro.
Ya ce mutanen yanki da makwabta sun dogara ne da sojojin domin ba su kariya inda yanzu hankulansu suka tashi bayan tattarewa da sojojin suka yi.
Ana zaton wannan janyewa na sojojin bai rasa nasaba da abin fashewa da ya rutsa da su wanda ya jawo rasa rayuwa.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata 23 ga watan Afrilu a kan hanyar Allawa zuwa Pandogari da ke karamar hukumar.
Sojoji 6 sun mutu a harin Neja
A wani labarin, wasu sojoji sun gamu da ajalinsu yayin da 'yan bindiga suka kai musu harin bazata a jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a kauyen Roro da ke jihar a makon da ya gabata inda da yawa daga sojojin suka samu raunuka.
Asali: Legit.ng