Fasinjoji 50 sun sha da kyar bayan tayar jirgin sama ta kama da wuta a Fatakwal

Fasinjoji 50 sun sha da kyar bayan tayar jirgin sama ta kama da wuta a Fatakwal

  • Fasinjoji 50 ne suka sha da kyar a filin sauka da tashin jiragen sama na Fatakwal bayan tayoyin jirgi sun kama da wuta
  • Jirgin na kamfanin Dana Airlines ya dawo kan layi ne bayan matukin jirgin ya fuskanci akwai matsala tattare dashi kafin su lula samaniya
  • Jami'an kashe gobara da na kiyaye hadurran jiragen sama sun gaggauta kai dauki inda a halin yanzu ake bincike kan musabbabin lamarin

Fatakwal, Rivers - A kalla fasinjoji 50 ne aka ceto bayan wuta ta kama da tayoyin jirgin saman kamfanin Dana Airlines Limited a Fatakwal.

Lamarin ya faru a ranar Litinin da yammaci a filin sauka da tashin jiragen sama na Fatakwal, jaridar Punch ta tabbatar da hakan.

An tattaro cewa, ba a rasa ko rai daya ba kuma babu fasinjan da ya samu rauni saboda ma'aikatan kwana-kwana da ke filin sauka da tashin jiragen saman sun gaggauta kai dauki.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Fasinjoji 50 sun sha da kyar bayan tayar jirgin sama ta kama da wuta a Fatakwal
Fasinjoji 50 sun sha da kyar bayan tayar jirgin sama ta kama da wuta a Fatakwal. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun Dana Airline, Kingsley Ezenwa ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar mai taken "Bayani kan al'amarin da ya faru a ranar 2/5/22 a jirgin sama a Fatakwal wanda ake bincika."

Channels TV ta ruwaito, wani bangaren takardar yace:

"Jirgin samanmu mai lamba 5N JOY da ke aiki da 9J 344 daga Fatakwal zuwa Legas a ranar 2 ga watan Maris 2022, ya shirya tashi yayin da matukin jirgin ya fuskanci wata matasala wacce ya bincika da hukumar kula da hadurran jiragen sama inda ya hanzarta dawowa kan layi kamar yadda dokar ayyukan ta bukata.
"Sai dai, illar birkin sakamakon fasa tashin da yayi ya shafi tayoyin jirgin wanda hakan yasa wuta ta tashi.
"Dukkan fasinjoji 50 da ke kan jirgin sun sauka lafiya kalau kuma tawagar kula da jirgin da gaggawa sun dakatar da shi har sai an kammala bincike.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

"Muna kara mika sakon ban hakuri ga dukkan fasinjojin da ke kan jirgin ko da kuwa sun shiga wata takura sakamakon soke tashin jirgin da aka yi."

Dakarun NAF da AIB sun mamaye wurin da jirgin sama yayi hatsari a Kaduna

A wani labari na daban, Sojoji sun rufe yankin da jirgin dakarun sojin saman Najeriya yayi hatsari a ranar Juma'a a filin suaka da tashin jiragen sama na Kaduna.

Jirgin saman wanda ke dauke da shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji ya fadi a filin jirgin inda ya kashe dukkan mutum 11 da ke ciki har da matukan jirgin.

A yayin jawabi kan lamarin, manajan filin jirgin sama na Kaduna, Amina Salami ta sanar da Channels TV cewa hukumar sojin Najeriya sun mamaye yankin da lamarin ya auku.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel